'Zama daram a Najeriya': Shoprite ta yi karin bayani a kan labarin janyewa daga Najeriya

'Zama daram a Najeriya': Shoprite ta yi karin bayani a kan labarin janyewa daga Najeriya

Chastex Consult, kamfanin manyan shagunan siyayyya na ShopRite, ya yi watsi da wani labari da kafafen yada labarai ke yadawa a kan cewa za su daina kasuwanci a Najeriya ta hanyar rufe shagunansu da ke fadin kasa.

Yayin hirarsa ta wayar tarho da jaridar Vanguard, darektan Chastex na kasa, Ini Archibong, ya bayyana cewa; "ShopRite ba zai bar Najeriya ba, kawai mun bawa 'yan kasuwar Najeriya damar saka hannu jari ne, kuma mun dade da fara tattaunawa dasu kafin yanzu.

"Babu inda za mu, waye zai saka hannun jarin biliyan $30 kuma ya rufe shago? labarin ya sabawa tunani mai kyau.

"Kawai mun bawa ma su son saka hannun jari 'yan Najeriya dama a kokarinmu na cimma manufarmu ta fadada kasuwanci a Najeriya. Babu inda za mu.

"Na sha yi wa mutane bayani bakin gwargwado. Kar jama'a su damu, babu gaskiya a cikin rahoton," a cewarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa shararren kamfanin nan na Shoprite masu katafaren shaguna a kasashen Afrika har da Najeriya, sun bada sanarwar cewa za su fice daga kasar nan.

Rahotanni sun ce bayan shekaru 15 su na kasuwanci a Najeriya, Shoprite za su bar Najeriya.

Kamfanin zai yi gwanjon kayan da ya rage masa kafin ya bar kasar.

'Zama daram a Najeriya': Shoprite ta yi karin bayani a kan labarin janyewa daga Najeriya
Shagon Shoprite
Asali: Facebook

Shoprite ya bada wannan sanarwa ne a ranar Litinin, 2 ga watan Agusta, 2020.

Hakan na zuwa ne bayan kamfanin ya fitar da bayanin yadda kasuwancinsa ya ke tafiya.

Rahoton kasuwancin Shoprite da ya fito karshen watan Yuni ya nuna cewa kamfanin kasar wajen ya na fuskantar kalubale wajen aiki a kasar Najeriya.

Kafin Shoprite, kamfanin Mr. Price da Woolworths sun bar Najeriya a baya. Duk wadannan kamfanonin kasar Afrika ta kudu ne da ake ji da su a Nahiyar nan.

DUBA WANNAN: 'Iyayena sun sallamani, sun ce kar na sake na koma gidansu' - Matashiyar da ta shiga fim

A jawabin da kamfanin ya fitar, ya ce sakamakon ribar kasuwancinsu ya nuna zamansu ya kare a Najeriya, hakan na nufin asarar da Shoprite ya ke yi, ya yi kamari.

Cinikin da kamfanin ya ke yi ya yi kasa da 1.4% daga shekarar 2018 zuwa yanzu.

Karancin cinikin kamfanin ya kara lalacewa sosai a lokacin da aka hana jama'a fita saboda annobar COVID-19.

A dalilin takunkumin COVID-19, sai da cinikin Shoprite ya yi kasa da 7.4%, ko da dai masu yi wa kamfanin ciniki su kan cika kwandonsu a wannan lokaci.

Wannan lamari zai iya sa dumbin mutane da su ke aiki da kamfanin su rasa sana’arsu. Watakila kuma barin Shoprite ya taimakawa wasu kamfanonin cikan gida.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel