Rauni game da shirye-shirye na barazana ga komawar ɗalibai a wannan mako

Rauni game da shirye-shirye na barazana ga komawar ɗalibai a wannan mako

Jihohi Najeriya a ranar Lahadi sun rarrabu dangane da damar da gwamnatin Tarayya ta bai wa ɗaliban ajin karshe ta komawa makarantu domin karasa shirin zana jarrabawar kammala karatun sakandire.

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin a buɗe makarantu a gobe Talata domin 'yan ajin karshe na makarantun sakandire su kammala shirinsu na zana jarrabawar WAEC wadda za a fara gudanarwa a ranar 17 ga watan Agusta.

Binciken da jaridar The Punch ta gudanar ya nuna cewa, ɗaliban aji shida a jihohin Legas, Benuwe, Kwara da Ogun, na shirye-shiryen komawa a ranar Talata yayin da na jihar Cross River sun koma a yau Litinin.

Har yanzu jihar Enugu, Gombe, da Ribas basu sanar da ranar komawar ɗalibansu ba, sabanin jihar Ekiti inda ɗaliban za su koma a ranar 10 ga watan Agusta.

Karamin ministan ilimi; Emeke Nwajiuba
Karamin ministan ilimi; Emeke Nwajiuba
Asali: Twitter

Binciken manema labarai ya nuna cewa, gwamnatocin jihohi da dama sun gaza tanadar wuraren wanke hannaye a karkashin ruwa mai gudana da kuma sunadarin tsaftace hannu kamar yadda aka shata ka'idodin komawa makarantun.

Ana iya tuna cewa, a yayin da karamin ministan ilimi Emeka Nwajiuba ke sanar da ranar buɗe makarantun, ya kuma bayyana karara cewa sai an kiyaye ka'idodin dakile yaduwar cutar korona yayin komawa.

A cewarsa, dole ne kowace makaranta ta tanadi ruwan wanke hannu da kuma sunadarin tsaftace hannu (sanitizer).

KARANTA KUMA: Atiku ya bukaci Buhari da APC su nemi afuwar ‘yan kasa kan nauyin bashin da suka dora wa Najeriya

Sai dai har ya zuwa ranar Lahadi, mafi akasarin gwamnatocin jihohi sun gaza cika dukkan ka'idojin da kwamitin shugaban kasa mai yaki da cutar korona a Najeriya ya shata.

Legit.ng ta ruwaito cewa, alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa NCDC na ranar 2 ga watan Agustan 2020 ya bayyana, karin mutum 304 sun kamu da cutar korona a Najeriya.

Jimillar masu cutar ta kai 43,841 a fadin kasar nan. Mutum 20,308 ne suka warke wasai daga jinyar cutar yayin da mutum 808 suka riga mu gidan gaskiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel