Wata kungiya ta tono tuggun tsige ministan shari'a na Najeriya

Wata kungiya ta tono tuggun tsige ministan shari'a na Najeriya

Wata kungiya mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa, IGAC (Integrity Group Against Corruption) ta tono tuggun da wasu mutane ke kulla wa domin tumbuke Lauyan koli kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami.

A cewar kungiyar IGAC, ta bankado wani sakon 'email' na wani mutum mai suna Olaruwanju Suraju, wanda ya ke ikirarin shugabancin wata kungiya mai yaki da cin hanci da rashawa.

A sakon da IGAC ta yakito, ta ce kungiyar da Suraju ya ke ikrirarin jagorancinta, ya nuna matsananciyar bukatar ganin an sauke Malami daga kujerarsa.

Shugaban kungiyar, Bello Gambo Iliya, shi ne ya yi wannan zargi a ranar Talata, 28 ga watan Yuli yayin da yake zantawa da manema labarai.

A cewar Gambo Iliya, makasudin sakon na 'email' mai dauke da kwanan watan ranar Litinin, 27 ga Yuli, shi ne neman tattaro magoya bayan ganin an tumbuke Malami daga mukaminsa.

Ministan Shari'a; Abubakar Malami
Ministan Shari'a; Abubakar Malami
Asali: Facebook

Ya ce manufar mawallafin sakon shi ne tattaro magoya bayan da zasu hurowa shugaban kasa Muhammadu Buhari wutar juya wa Ministansa baya.

A dalilin haka ne Mista Gambo ya ke kira ga Malami a kan ya ci gaba da tsayuwar daka a kan akidar yaki da rashawa da ya sanya a gaba.

Legit.ng ta kuma ruwaito cewa an saki Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho (PRTT) da tsohon shugaban kasa Jonathan ya kafa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya bayyana cewa an saki Maina ne bayan ya shafe wata tara a tsare kamar yadda ta sanar da hakan a cikin rahoton da ta wallafa da yammacin ranar Talata.

A ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2019 EFCC ta gurfanar da Maina tare da dansa, Faisal, da wani kamfani; 'Common Input Property and Investment Ltd', a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja.

KARANTA KUMA: An cafke mutane 244 da suka yi yunƙurin yin aikin Hajji ta ɓarauniyar hanya

Da ya ke tabbatar da hakan yayin hirarsa ta wayar tarho da NAN a ranar Talata, Adeola Adedipe, lauyan Maina, ya bayyana cewa an saki Maina da yammacin ranar Litinin bayan ya kammala cika ka'idojin samun 'yanci.

Lauya Adipe, wanda ke aiki a karkashin ofishin babban lauya Ahmed Raji (SAN), ya ce tun ranar 24 ga watan Yuli ya kamata a saki Maina amma wasu 'yan al'amura suka kawo tsaiko zuwa ranar 27 ga watan Yuli.

Da ya ke amsa tambaya a kan dalilin da yasa aka ci gaba da tsare Maina bayan mai shari'a, Jastis Abang, ya sassauta sharudan bayar da belinsa a ranar 29 ga watan Yuni, lauyan ya ce: "an dan samu tsaiko wajen bin wasu hanyoyi da ka'idojin aiki."

Sai dai, Lauyan ya musanta cewa jami'an gwamnati sun kawo tsaiko da gan-gan domin ramuwar gayya a kan Maina.

Kazalika, Afam Osigwe, wani lauya daga cikin tawagar lauyoyin da ke kare Maina, ya tabbatar da cewa Maina ya koma gida cikin iyalinsa tun yammacin ranar Litinin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel