Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 40,000 - NCDC

Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 40,000 - NCDC

Sakamakon bincike ya nuna cewa, cutar korona ta yadu a duk jihohi 36 na Najeriya da kuma babban birnin kasar bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar karo na farko a kasar.

Hakan ya na kunshe ne a cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Lahadi, 27 ga watan Yuli.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Cross River.

Yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 14,456 sai mutum 2,087 da suka warke, yayin da kuma mutum 192 suka kwanta dama.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Kawo yanzu a duk fadin kasar, cutar ta harbi mutum 40,532 sai kuma mutum 17,374 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 858 da suka riga mu gidan gaskiya.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 266,323 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 22,300 kacal ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

KARANTA KUMA: Sanatan Kano ta Tsakiya zai fitar da matasan 'yan kwallo 5 zuwa kasashen ketare

Da misalin karfe 10.48 na ranar Lahadi da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 555 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 600 da cutar ta harba cikin jihohi 18 sun kasance kamar haka: Lagos(156), Kano(65), Ogun(57), Filato(54), Oyo(53), Benuee(43), Abuja(30), Ondo(18), Kaduna(16), Akwa Ibom(13), Gombe(13), Ribas(12), Ekiti(9), Osun(8), Cross River(3), Borno(2), Edo(2), Bayelsa(1)

Baya ga jihar Legas da ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu da mutum 3,481 yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku da mutum 2,570.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba da kuma wadanda suka mutu cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos: Kamuwa - 14,456 Mutuwa - 192

Abuja: Kamuwa - 3,481 Mutuwa - 41

Oyo: Kamuwa - 2,570 Mutuwa - 24

Edo: Kamuwa - 2,167 Mutuwa - 77

Rivers: Kamuwa - 1,652 Mutuwa - 52

Kano: Kamuwa - 1,520 Mutuwa - 53

Delta: Kamuwa - 1,464 Mutuwa - 40

Kaduna: Kamuwa - 1,365 Mutuwa - 12

Ogun: Kamuwa - 1,301 Mutuwa - 23

Ondo: Kamuwa - 1,061 Mutuwa - 22

Filato: Kamuwa - 834 Mutuwa - 19

Ebonyi: Kamuwa - 759 Mutuwa - 24

Enugu: Kamuwa - 741 Mutuwa - 17

Katsina: Kamuwa - 733 Mutuwa - 23

Kwara: Kamuwa - 711 Mutuwa - 16

Borno: Kamuwa - 611 Mutuwa - 35

Gombe: Kamuwa - 571 Mutuwa - 23

Bauchi: Kamuwa - 538 Mutuwa - 13

Abia: Kamuwa - 536 Mutuwa - 4

Imo: Kamuwa - 465 Mutuwa - 9

Osun: Kamuwa - 443 Mutuwa - 10

Benue: Kamuwa - 337 Mutuwa - 6

Bayelsa: Kamuwa - 327 Mutuwa - 21

Jigawa: Kamuwa - 322 Mutuwa - 11

Nasarawa: Kamuwa - 308 Mutuwa - 8

Akwa Ibom: Kamuwa - 221 Mutuwa - 7

Neja: Kamuwa - 168 Mutuwa - 12

Sokoto: Kamuwa - 153 Mutuwa - 16

Adamawa: Kamuwa - 140 Mutuwa - 9

Anambra: Kamuwa - 132 Mutuwa - 12

Ekiti: Kamuwa - 113 Mutuwa - 2

Kebbi: Kamuwa - 90 Mutuwa - 7

Zamfara: Kamuwa - 77 Mutuwa - 5

Yobe: Kamuwa - 66 Mutuwa - 8

Taraba: Kamuwa - 54 Mutuwa - 0

Cross River: Kamuwa - 40 Mutuwa - 3

Kogi: Kamuwa - 5 Mutuwa - 2

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel