Yan bindiga sun kashe lauya a Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa

Yan bindiga sun kashe lauya a Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa

- Yan bindiga sun kashe lauya mazaunin jihar Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa

- Dan uwan mamacin ya ce 'yan bindigar sun fara harbin kaninsa ne a kafada, a lokacin da yayi kokarin guduwa kuma suka harbe shi a baya

- Sai dai har yanzu rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna bata tabbatar da faruwar lamarin ba

Yan bindiga sun kashe wani lauya mazaunin Kaduna, Haro Gandu, yayin da suka yi garkuwa da matarsa da kuma yaronsa, a gidansa da ke Tollgate, karamar hukumar Chikun, jihar Kaduna.

Gandu ya kasance ma'aikaci ne a ma'aikatar shari'a, an kashe ni bayan da 'yan bindigan suka afka gidansa a daren ranar Lahadi.

Timothy Gandu, tsohon kwamishin tsara tattalin arziki, kuma dan uwan mamacin, ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin.

A cewarsa, 'yan bindigar sun shiga gidan ne da karfin tsiya bayan da suka balle daya daga cikin tagogin gidan.

Tsohon kwamishinan ya ce 'yan bindigar sun fara harbin kaninsa ne a kafada, a lokacin da yayi kokarin guduwa kuma suka harbe shi a baya.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta kara wa'adin janye dokar ta baci kashi na biyu

Yan bindiga sun kashe lauya a Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa
Yan bindiga sun kashe lauya a Kaduna, sun tafi da matarsa da yaronsa
Asali: Depositphotos

Gandu ya ce bayan da aka kashe shi, 'yan bindigar suka tafi da matarsa da yaronsa.

Ya ce, "Sunzo gidan ne a daren ranar Lahadi, suka balle taga daya sannan suka shiga gidan.

"Sun fara harbin kafadarsa, ya yi kokarin mutuwa, suka bishi, suka harbe shi a baya, a nan take ya mutu. Sun yi awon gaba da matarsa da yaronsa.

"Kusan dai labarin ta'addancin da ke faruwa ke nan a ko ina. Yan bindiga na shiga gidaje suna kisa da garkuwa da jama'a."

Sai dai har zuwa lokacin wallafa wannan labarin, rundunar 'yan sanda ta jihar bata tabbatar da lamarin ba.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya ce zai tuntubi D.P.O na ofishin ofishin da lamarin ya faru domin tabbatar da rahoton.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel