Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa'adin neman aikin N-Power zuwa mako biyu

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa'adin neman aikin N-Power zuwa mako biyu

Gwamnatin Tarayya ta tsawaito lokacin da za ta rufe karbar rajistar rukuni na uku na masu neman aikin shirin N-Power har zuwa tsawon mako biyu.

Shigar da rajistar neman aikin N-Power ta hanyar yanar gizo an fara ta ne tun daga ranar 26 ga watan Yunin 2020 kuma aka kayyade za a rufe a ranar Lahadi, 26 ga watan Yuli.

Sai dai a yanzu gwamnatin ta yi tala-tala ga masu neman aiki a shirin na rage raɗaɗin talauci a Najeriya da cewar an kara mako biyu a kan ranar da ta kayyade a baya.

Gwamnatin ta sanar da cewa, ta kara tsawon makonni biyu ne domin bai wa matasa damar shigar da bukatun neman aiki a shiri na tallafa wa wadanda suka kammala karatu kuma ba su da aikin yi.

Har ila yau gwamnatin ta ce yawan adadin matasan da suka yi rajistar neman aikin ya zuwa yanzu, ya nuna azama da farin cikinsu ta neman samun shiga wannan shirin.

Sadiya Umar Farouq
Sadiya Umar Farouq
Asali: Twitter

A cewar gwamnatin, shirin zai dauki mutum 400,000 da za su yi aiki a bangarori da dama da suka hada da noma da lafiya da koyarwa da gine-gine da kuma fasaha.

Sanarwar tsawaita lokacin da za a rufe shigar da rajistar ta fito ne cikin wani sako da ministar agaji, bala'o'i da ci gaban al'umma, Sadiya Umar Farouq ta wallafa kan shafinta na Twitter a daren jiya na Lahadi.

Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari, ta yi karin haske game da biyan Naira dubu sittin ga masu cin moriyar shirin N-Power da ake daf da sallama.

Gwamnatin tarayyar ta ce ba za ta biya N60,000 ba a matsayin kudin sallama ga matasan da suka ci moriyar shirin N-Power kamar yadda suka bukata ba.

A ranar Juma'a ne wasu daga cikin matasan da suka ci moriyar shirin N-Power suka gudanar da zanga-zanga a gaban majalisar dokokin tarayya da ke birnin Abuja.

Kamar yadda Gidan Rediyon Freedom ya ruwaito, matasan sun nemi gwamnatin da ta biya su kudin sallama na naira dubu sittin tare da mayar da su ma'aikata na dindindin.

KARANTA KUMA: 'Dan kasuwa ya mutu a hannun 'yan sanda bayan kwanaki 6 ba tare da an gurfanar da shi a kotu ba

Matasan sun kuma ja hankalin gwamnatin a kan ministan kula da agaji, bala'o'i da ci gaban al'umma, Sadiya Umar Farouq, da ta sauka daga mukaminta.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ma'aikatar Rhoda Shaku iliya ta fitar, ta ce gwamnatin za ta kashe biliyoyin nairori wajen wajen ci gaba da wanzuwar shirin yayin da nan gaba za ta sake daukan wani sabon rukuni na matasa.

Rhoda ta ce bukatar matasan ba ta cikin tsarin shirin na N-Power da aka kaddamar tun fil a zal, kuma babu wani tanadi da gwamnatin ta yi na sallamar matasan domin daukan wani rukunin na daban.

Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin ba za ta bayar da kyautar kudin da matasan suka bukata ba wanda sun tasarma naira biliyan dari 300.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel