COVID-19: Sultan ya yi kira ga musulmi suyi sallar Idi a masallatan Juma'a

COVID-19: Sultan ya yi kira ga musulmi suyi sallar Idi a masallatan Juma'a

- Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar ya aike wa da musulmin Najeriya sabon sako gabanin babban sallah

- Sultan Abubakar ya bukaci limamai a sassan kasar suyi sallar Idin a masallatan Juma'a a maimakon zuwa filayen Idi

- Ya kuma sanar da cewa a ranar Juma'a 31 ga watan Yuli ne da ya yi daidai da 10 ga watan Zulhijja ta 1441 AH za ayi babbar sallan

Sarkin Musulimi Sa'ad Abubakar ya bukaci hakimai da shugabannin addini suyi limancin sallar Idi a masallatan Juma'a a maimakon zuwa filayen sallar Idi.

Sultan din ya bayar da wannan shawarar ce yayin da ya ke sanar da cewa a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 2020 ce ranar babbar Sallah kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba 22 ga watan Yuli, Sultan Abubakar ya yi kira ga alummar musulmi suyi adduo'in zaman lafiya da samun cigaba a kasar.

Sultan ya sanar da ranar babbar sallah, ya yi kira ga musulmi suyi sallah a masalltan Juma'a
Sultan ya sanar da ranar babbar sallah, ya yi kira ga musulmi suyi sallah a masalltan Juma'a
Asali: Twitter

"Mai alfarma, Alhaji Muhammad Saad Abubakar CFR, mni, Sultan din Sokoto kuma shugaban Kwamitin Koli ta Musulunci ta Najeriya, NSCIA, ya sanar da cewa ranar Juma'a 31 ga watan Yulin 2020 da ya yi daidai da ranar 10 ga watan Zulhijja ta 1441 AH ne za ayi babbar sallar wannan shekarar," in ji sanarwar.

DUBA WANNAN: An bawa Sarkin Shinkafi wa'addin awa 24 ya kwace sarautar da ya bawa Fani-Kayode

"Bugu da kari, duba da halin da ake ciki na annobar Covid 19, Sultan yana shawartar dukkan hakimai da Limamai a jihar Sokoto suyi sallar Idi a masallatan Juma'a da ke garuruwansu da maimakon filayen Idi.

"Kazalika, Majalisar Kolin tana shawartar sauran musulmi a dukkan sassan kasar suyi sallar Idi a masallatan Juma'a domin taimakawa wurin dakile yaduwar annobar Covid 19.

"Mai Alfarma Sultan yana taya yan Najeriya farin ciki kuma yana musu adduar Allah ya yi musu albarka. Ya kuma bukaci musulmin Najeriya su cigaba da yin adduo'in samun zaman lafiya da cigaba kana yana taya su murnar salla babba. Da fatan Allah ya amshi ibadun mu. amin."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel