Hotunan cikin otal na farko a duniya da aka kawata da zinari
Otal na Dolce Hanoi Golden Lake da ke Vietnam ya bayyana a matsayin otal na farko a duniya da aka yi wa fenti da zinari.

Asali: Getty Images
Ba a dade da bude otal din ba don masu ziyara. An bayyana kayan alatun da ke cikinsa inda da yawa daga cikinsu aka kawata su da zinari. Daga cikin akwai kwamin wanka na zinari, masai na zinari da ababen cin abinci na zinari.

Asali: Getty Images
Babban otal din na nan a kusa da tafkin Giang Vo a tsakiyar garin Hanoi, babban birnin Vietnam.

Asali: Getty Images
An gano cewa otal din an malala masa zinarin bayan kwashe shekaru 11 da aka yi ana gininsa.

Asali: Getty Images
Yana da dakuna 400 tare da bene mai hawa 25. Yana karkashin American Wyndham Hotels. An ware wasu dakuna na daban da ake bada hayarsu a farashin pam 5,200.

Asali: Getty Images
A ranar wata Alhamis, yayin bude otal din, an nuna kwamin wanka tare da kofunan shan ruwa na zinari.

Asali: Getty Images

Asali: Getty Images
An gano cewa a duk kwana daya ana biyan $250 yayin da ake bada hayar wasu dakuna $6,500.

Asali: Getty Images
An gano cewa an yi amfani da $200 miliyan don gina otal din.

Asali: Getty Images
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng