Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 543 sun kamu da cutar COVID-19 a Nigeria

Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 543 sun kamu da cutar COVID-19 a Nigeria

Kamar yadda Legit.ng Hausa ke kawo maku rahotanni daga hukumar dakile yaduwar cutuka ta Nigeria, NCDC, musamman kan annobar COVID-19. A yau Laraba, 22 ga watan Yulin 2020, hukumar ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, sabbin mutane 543 sun kamu da cutar COVID-19.

Ga jadawalin mutanen da suka kamu da cutar, jiha bayan jiha.

Lagos-180

FCT-86

Kaduna-56

Edo-47

Ondo-37

Kwara-35

Ogun-19

Rivers-19

Kano-17

Ebonyi-16

Enugu-16

Delta-7

Bayelsa-4

Bauchi-3

Abia-1

Kamar yadda hukumar ta wallafa, a yanzu akwai tabbacin mutane 38,344 masu dauke da cutar kuma suna samun kulawa daga likitoci.

Haka zalika, akwai adadin mutane 15,815 da aka sallama bayan samun tabbacin sun warke daga cutar.

A hannu daya kuwa, mutane 813 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar COVID-19.

A wani labarin kuwa; Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da kisan gillar da mayakan Boko Haram sukayiwa ma'aikatan hukumar bada agajin gaggawa SEMA guda biyar a jihar Borno.

Kusan wata daya ke nan da mayakan Boko Haram suka yi garkuwa da ma'aikatan.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba ta hannun Garba Shehu, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan ma'aikatan da suka ransu.

Shugaban kasar, wanda ya roki Allah ya ba iyalan juriyar wannan babban rashi da suka yi, ya kuma tabbatarwa iyalan cewa gwamnatinsa zata ci gaba da yin duk mai yiyuwa don ganin ta kawo karshen Boko Haram.

Shugaba Buhari ya kuma jajantawa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar SEMA, wadanda mummunar waki'ar ta fada kansu.

Buhari, ya gode masu akan jajircewar da suke yi kullum wajen kai tallafi ga wadanda harin Boko Haram ya shafa a Arewa maso Gabas.

A wani labarin makamancin wannan, Majalisar zartaswa ta kasa (FEC) ta amince da ware N75bn domin samar da shiri na musamman da zai tallafawa matasan kasar, da nufin bunkasa rayuwarsu.

Ministan matasa da waanni, Sunday Dare ya bayyana hakan ga 'yan jaridun fadar shugaban kasa, bayan fitowa daga taron majalisar zartaswar da aka shafe awanni takwas ana yinsa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci zaman majalisar zartaswar.

A cewarsa, wadanda ke a cikin shekarun samartaka kuma masu tsarin kasuwanci na gaskiya kuma suke zaune a kusa da inda aka gina bankunan 'yan kasuwa 125 a fadin kasar, kuma suka cancanta ne kawai zasu ci gajiyar tallafin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel