Da duminsa: Mutane 562 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a Nigeria

Da duminsa: Mutane 562 sun sake kamuwa da cutar COVID-19 a Nigeria

Kamar yadda alkalumman hukumar yaki da cutuka masu yaduwa (NCDC), ya bayyana na ranar Litinin, 20 ga watan Yulin 2020, sabbin mutum 562 sun sake kamuwa da korona a Najeriya.

Ga bayani daki-daki, jiha bayan jiha.

FCT-102

Lagos-100

Plateau-52

Kwara-50

Abia-47

Kaduna-35

Benue-34

Oyo-26

Ebonyi-24

Kano-16

Niger-15

Anambra-14

Gombe-12

Edo-11

Rivers-6

Nasarawa-5

Delta-5

Borno-3

Enugu- 2

Bauchi-2

Kebbi- 1

Kamar yadda hukumar NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter, a yanzu jimillar mutane 37,225 ne ke dauke da cutar wadanda kuma suke kwance a gadon asibiti.

Haka zalika, hukumar ta sanar da cewa, akwai jimillar mutane 15,333 da aka sallama daga asibiti bayan samun tabbacin warkewa daga cutar.

A hannu daya kuma jimillar mutane 801 ne suka mutu sakamakon wannan cutar.

A wani labarin kuwa, Mallam Ismaila Isa Funtua, makusancin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rasu a daren yau, Litinin, 20 ga watan Yuli.

Mariga Funtua ne manajan darektan kamfanin jaridar 'Democrat' na farko, sannan ya taba rike shugaban kungiyar masu kamfanin jarida a Najeriya (NPAN).

Jaridar 'ThisDay' ta rawaito cewa Funtua ya mutu ne sakamakon ciwon zuciya.

Ita kuwa jaridar Daily Trust ta ruwaito kanin mamacin da aka sakaya sunansa, yana cewa: "Mallam ya shaidawa iyalansa cewa yana son ganin likitansa amma ya fara zuwa wajen mai yi masa aski.

"Shine ya tuka motar da kansa har zuwa asibiti bayan barin shagon mai askin," a cewar kanin.

Rahotanni sun bayyana cewa an ajiye gawar marigayin a masallacin Area 1, inda za a sallace shi a safiyar ranar Talata.

Ismaila Isah ya kasance mashahurin dan kasuwa, wanda ya mallaki ilimin gudanar da kasuwanci na sama da shekaru 30.

Ya taba kasancewa shugaban kamfanin sarrafa auduga na UNTL, wanda ya dauki ma'aikata sama da dubu goma aiki, kuma ya taba kasancewa ministan kasar Nigeria.

Shine wanda ya samar da kamfanin gine gine na Bulet International Nigeria Limited (kamfani mafi girma wanda 'yan asalin Nigeria ke tafiyar da shi), wanda kuma ya gina mafi yawan manyan gine ginen da ke cikin Abuja.

Har ya zuwa mutuwarsa, marigayi Funtua na daga cikin dattijai a kungiyar NPAN, sannan shine shugaban kamfanin gine - gine mai suna 'Bulet Construction Company'.

Za a yi jana'izarsa da safiyar ranar Talata bisa tsarin addinin Musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel