Harin da 'yan bindiga suka kai mana a Katsina dakaru 3 ne kawai suka mutu - Rundunar Soji

Harin da 'yan bindiga suka kai mana a Katsina dakaru 3 ne kawai suka mutu - Rundunar Soji

Rundunar sojin Najeriya ta yi karin haske dangane da asarar da ta yi a hannun 'yan daban daji yayin da suka kai wa dakarunta hari a karamar hukumar jibiya ta jihar Katsina.

Kafofin labarai da dama sun ruwaito cewa, harin da 'yan bindiga suka kai wa wata rundunar sojin kasa a jihar Katsina, ya salwantar da rayukan dakaru 16.

Sai dai da take mayar da martani da fayyace ainihin asarar da harin ya janyo mata, rundunar sojin ta ce dakarunta 3 ne kacal suka riga mu gidan gaskiya

Cikin wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta fitar a ranar Lahadi, ta ce dakarun Operation Sahel Sanity, sun kashe akalla 'yan daban daji 17 yayin wata arangama a karamar hukumar Jibiya ta jihar Katsina.

Dakarun Sojin Najeriya
Hoto daga jaridar Premium Times
Dakarun Sojin Najeriya Hoto daga jaridar Premium Times
Asali: Twitter

Hukumar tsaron ta kuma ce dakarunta sun samu nasarar kwato muggan makamai da suka hadar da bindigu kirar AK 47, alburusai da kuma babura bakwai bayan sun fafata da 'yan ta'adda.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar Operation Sahel Sanity, Bernard Onyeuko ya sanar, an yi asarar rayukan dakaru uku yayin da kuma wasu dakarun hudu suka jikkata a filin daga.

Sai dai wannan ikirari da rundunar sojin ta yi ya saba wa rahoton da wani babban jami'in soji ya gabatar wa manema labarai na jaridar Premium Times.

Majiyar mai tabbas ta sanar da cewa, akalla rayukan sojoji 16 ne suka salwanta ciki har da wasu manyan dakaru 3 yayin da wasu 28 suka jikkata a harin na kwanton bauna da 'yan ta'adda suka kai a ranar Asabar.

Legit.ng ta ruwaito cewa, A wani simame da 'yan daban daji suka kai jihar Katsina a ranar Asabar, sun salwantar da rayukan dakarun soji 16, yayin da 28 suka jikkata.

KARANTA KUMA: Zaben Ondo: Mutum 4 sun janye wa Akeredolu takara yayin da aka fara zaben fidda gwani

Da misalin karfe 6.13 na Yammacin ranar Asabar yayin da dakaru suka fita sintiri a yankin Shimfida na karamar hukumar Jibiya ta jihar, 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna, inda suka rika yi musu ruwan wuta daga wani saman tsauni.

Daga cikin dakarun da suka riga mu gidan gaskiya sun hadar da Manjo, Kyaftin, da Laftanar kamar yadda wata majiya daga dakarun sojin ta shaidawa manema labarai na jaridar The Punch.

An tattaro cewa wasu 'yan ta'adda biyu sun raunata yayin da dakarun sojin suka yi yunkurin mayar da martani.

Sai dai yayin da aka tuntubi kakakin rundunar sojin kasa, Kanal Sagir Musa, ya ce ba zai iya bayar da tabbaci ba kuma ba ya da ta cewa domin lokacin shi ne karo na farko da ya samu labarin harin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel