Pondei ba zai sake bayyana gaban kwamitin bincike ba - Gbajabiamila

Pondei ba zai sake bayyana gaban kwamitin bincike ba - Gbajabiamila

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa mukaddashin manajan daraktan hukumar kula da ci gaban yankin Neja Delta, Kemebradikumo Pondei, wanda ya yanke jiki ya fadi yayin bincike, ba zai sake bayyana a gaban kwamitin ba.

Kakakin ya bayyana hakan ne bayan da aka koma zaman majalisar wanda aka dakatar bayan faduwar Pondei. Ya ce kwamitin zai karanta rubutaccen rahoton manajan daraktan.

Gbajabiamila ya yi wannan martanin ne bayan da shugaban NDDC ya fadi kuma aka garzaya da shi asibiti.

"Babu bukatar manajan daraktan NDDC ya sake bayyana a gaban kwamitin tunda yana da rubutaccen rahoton.

"Ina yi wa Pondei fatan samun lafiya kuma na tura daraktan lafiya na majalisar tarayya da ya je don ganin halin da yake ciki," yace.

KU KARANTA: Boko Haram: Modu Sulum, sabon kwamanda mai matukar hatsari

A makon jiya ne kwamitin majalisar ya fara gayyatar tsofin shugabanni da ma su ci yanzu a hukumar NDDC domin amsa tambayoyi a kan badakalar da ake zargin ana tafkawa a hukumar.

Honarabul Tunji - Ojo, ya sanar da yin murabus dinsa ne ranar Litinin yayin zaman kwamitin domin cigaba da gudanar da binciken badakala a hukumar NDDC.

Kwamitin majalisar ya kira Akpabio ne bayan da Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar, ta bayyana wasu zarge-zarge a kan shi a ranar Juma'a.

A ranar Alhamis din makon jiya ne Pondei ya jagoranci mukarrabansa wajen ficewa daga dakin da kwamitin majalisa ke yi ma sa tambayoyi a kan zargin badakala a hukumar NDDC.

Murabus din dan majalisar ba zata rasa nasaba da zarginsa da cin hanci da Mista Pondei ya yi ba a makon jiya.

Da ya ke bayyana dalilinsa na ficewa daga wurin zaman kwamitin bincike da majalisa ta kafa, Mista Pondei ya bayyana cewa ba zai yi magana a gaban kwamitin da ake zargin shugabansa da cin hanci ba.

Sauran mambobin kwamitin sun bayyana amincewarsu da shugabancin Honarabul Tuni - Oyo. Kazalika, sun bukaci Mista Pondei da ministan yankin Neja - Delta, Sanata Godswill Akpabio, su bayyana a gaban kwamitin ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel