El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki

El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki

Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci ma'aikatan jihar Kaduna su koma bakin aiki ranar Litinin, 20 ga Yuli bayan kwashe watanni uku sun zaune a gida sakamakon bullar cutar Coronavirus.

Gwamnatin ta sa dokar kulle tun ranar 26 ga Maris, 2020.

A takardar da ta fito daga ofishin shugaban ma'aikatan jihar, an zabawa kowani sashen ma'aikata ranakun da zasu rika zuwa aiki daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana.

Takardar da Sakataren din-din-din na ofishin shugaban ma'aikata, Ibrahim Jere, ya rattafa hannun, an umurci dukkan diraktoci, sakatarorin da manya jami'ai su rika zuwa daga ranar Litinin zuwa Juma'a.

Amma ma'aikatan da ke daraja ta 14 zuwa sama za su rika zuwa aiki cikin kwanaki uku; Litinin, Laraba da Juma'a.

Su kuma ma'aikata dake daraja ta 7 zuwa 13 zasu rika zuwa aiki ranar Talata da Laraba kacal.

Bugu da kari, domin takaita yiwuwar yaduwar cutar Korona a ma'aikatun, za'a hana baki ziyara kuma za'a tantance kowani ma'aikaci kulli yaumin tsakanin karfe 8:30 zuwa 9:30 kafin shiga aiki.

Hakazalika za'a tabbatar da bin sharruda irinsu bada tazara, duba zafin jiki, tsafta, wanke hannu da sauran su.

Tun kan a bude Masallatai, El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki
El-Rufa'i ya umurci ma'aikatan gwamnati su koma bakin aiki
Asali: UGC

A ranar 15 ga Yuni, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bayan sassauta dokar kulle da yayi a jihar Kaduna, mataki na gaba shine kiyaye yaduwar annobar korona wacce take hannun mutanen jihar.

El-Rufai ya roki jama'ar jihar da su dauki dawainiyar yaki da yaduwar cutar korona. Ya ce kada a mayar da kokarin da yayi a baya ta hanyar kin kiyaye dokokin hana yaduwar cutar.

Gwamnan ya mika sakon godiyarsa ga jama'ar jihar Kaduna a kan yadda suka yi hakurin watanni biyu da rabi wurin dakile annobar.

Gwamnan ya ce za a iya kara bude kasuwanci amma matukar an samar da na'urar gwada dumin jiki, sinadarin tsaftace hannu da kuma kiyaye dokar nesa-nesa da juna.

A yanzu dai Sallar Juma'a kadai ake yi a Masallatai kuma Kasuwanni na rufe.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

https://youtu.be/oSMy5yNO3qE

Asali: Legit.ng

Online view pixel