Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19

Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19

Blessing David, matashiya mai shekaru 19, wacce ta zama mamba a wata kungiyar asiri da ke jihar Edo, ta bayyana yadda maza 10 suka yi lalata da ita yayin rantsuwar shiga kungiyar.

David, wacce ta shiga kungiyar a 2019, ta bayyana cewa ta kwanta da mazan ne saboda rantsuwar zama mamba a kungiyar.

Matashiyar ta bayyana hakan ne a hedkwatar 'yan sanda da ke Edo yayin da kwamishinan 'yan sanda Babatunde Kokumo ya damkesu.

Kokumo ya kama wasu mutum 15 da ake zargi da fashi da makami, 'yan kungiyar asiri 6, masu garkuwa da mutane 3 da masu kisan kai hudu.

Shugaban 'yan sandan ya ce an kashe wasu mutum biyu da ake zargi da fashi da makami a sa'o'in farko na ranar Alhamis.

Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19
Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19. Hoto daga The Punch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda na dinga karuwanci da juna biyu sannan da sanin mijina - Matar aure

A wani labari na daban, tubabbiyar karuwa, Purity Wanjiru mai shekaru 25 a garin Nairobi a kasar Kenya ta bayyana abubuwan da ta fuskanta yayin da take titi.

Ta ce a wani lokaci da ya gabata tayi aure kuma ta zauna tare da mijinta wanda ta kwatanta da miji mara kula.

Ta ce ya san tana karuwanci amma bai taba hana ta ba ko kuma ya nuna damuwarsa. Hatta lokacin da take da ciki, ta ci gaba da karuwancinta a titi. Mijinta bai damu da hakan ba don bai ce komai a kai ba.

Wanjiru, wacce aka haifa a Uthiru da ke yankin Kiambu, ta tuna yadda ta koma titi bayan da ta samu rashin jituwa tsakaninta da iyayenta. Ta kwatanta yarintarta da wacce ke cike da tawaye ga iyayenta, wanda hakan yasa basu jituwa.

Hakazalika, karatunta kwata-kwata bai yi zurfi ba. Ta tuna yadda bata iya wuni daya a makaranta domin tana jin bukatar fita yawo a titi. Tun tana makarantar firamare, tana barin aji ta tafi yawo.

A yayin da take aji biyar, an dakatar da ita a makaranta tare da umarnin cewa sai ta sauya halayyarta za a amince da ita.

"A gidanmu mu 12 ne. Akwai wani lokaci da yayyina suka taru suka min duka saboda ni ce auta kuma ina nuna halin rashin son karatu. Ina da shekaru 13 na gudu na bar gida," tace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel