Adadin mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 35,000 - NCDC

Adadin mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 35,000 - NCDC

Bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 36 da kuma babban babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Juma'a, 17 ga watan Yuli.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Cross River.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 13,226 sai kuma mutum 1,958 da suka warke, yayin da mutum 176 suka kwanta dama.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Kawo yanzu a duk fadin kasar, cutar ta harbi mutum 35,454, sai kuma mutum 14,633 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 772 da suka riga mu gidan gaskiya.

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 206,422 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 20,049 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Da misalin karfe 11.48 na ranar Juma'a da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 600 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Da duminsa: WAEC da Najeriya an cimma matsaya, an dage ranar fara jarabawa

Sabbin mutane 600 da cutar ta harba cikin jihohi 20 sun kasance kamar haka: Lagos(129), FCT(118), Oyo(87), Kano(55), Benue(42), Enugu(35), Kwara(28), Imo(16), Ogun(13), Kaduna(12), Ondo(12), Delta(11), Edo(11), Plateau(8), Nasarawa(6), Ekiti(6), Niger(6), Borno(4), Abia(4), Gombe(3).

Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu da mutum 2,879 yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku da mutum 2,076.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:

Lagos: Kamuwa - 13,226 Mutuwa - 176

Abuja: Kamuwa - 2,879 Mutuwa - 39

Oyo: Kamuwa - 2,076 Mutuwa - 19

Edo: Kamuwa - 1,885 Mutuwa - 62

Ribas: Kamuwa - 1,480 Mutuwa - 47

Delta: Kamuwa - 1,415 Mutuwa - 37

Kano: Kamuwa - 1,386 Mutuwa - 53

Ogun: Kamuwa - 1,159 Mutuwa - 22

Kaduna: Kamuwa - 1,099 Mutuwa - 12

Ondo: Kamuwa - 877 Mutuwa - 21

Katsina: Kamuwa - 669 Mutuwa - 23

Ebonyi: Kamuwa - 646 Mutuwa - 10

Filato: Kamuwa - 603 Mutuwa - 16

Borno: Kamuwa - 597 Mutuwa - 35

Enugu: Kamuwa - 595 Mutuwa - 16

Gombe: Kamuwa - 540 Mutuwa - 22

Bauchi: Kamuwa - 522 Mutuwa - 13

Abia: Kamuwa - 460 Mutuwa - 3

Kwara: Kamuwa - 450 Mutuwa - 14

Imo: Kamuwa - 436 Mutuwa - 9

Osun: Kamuwa - 328 Mutuwa - 9

Jigawa: Kamuwa - 322 Mutuwa - 11

Bayelsa: Kamuwa - 318 Mutuwa - 20

Nasarawa: Kamuwa - 254 Mutuwa - 8

Benue: Kamuwa - 185 Mutuwa - 6

Akwa Ibom: Kamuwa - 162 Mutuwa - 3

Sokoto: Kamuwa - 153 Mutuwa - 16

Niger: Kamuwa - 151 Mutuwa - 7

Anambra: Kamuwa - 118 Mutuwa - 10

Adamawa: Kamuwa - 111 Mutuwa - 8

Kebbi: Kamuwa - 88 Mutuwa - 7

Ekiti: Kamuwa - 78 Mutuwa - 2

Zamfara: Kamuwa - 76 Mutuwa - 5

Yobe: Kamuwa - 63 Mutuwa - 8

Taraba: Kamuwa - 30 Mutuwa - 0

Cross River: Kamuwa - 12 Mutuwa - 1

Kogi: Kamuwa - 5 Mutuwa - 2

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel