Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa

Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa

Majalisar wakilan Najeriya ta bada umarnin damko mukaddashin manajan daraktan kwamitin rikon kwarya na hukumar habaka yankin Neja Delta, Farfesa Kemebradikumo Pondei a kan yadda ya fice daga majalisar babu izini.

Idan za mu tuna, ana bincikar pondei ne a kan wasu miliyan N40 da suka yi batan dabo a hukumar, ya fice daga majalisar a ranar Alhamis yayin da ake bukatar jin ta bakinsa.

Shugaban NDDC ya zargi shugaban kwamitin majalisar wakilan masu alhakin bincikarsu, Olubunmi Tunji-Ojo, da rashawa.

Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kallabi tsakanin rawuna: Abubuwa 10 da ba a sani ba game da Arotile

Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

A yayin jawabi ga kwamitin, Pondei ya ce, "Mu a NDDC ba mu amince da shugaban kwamitin binciken nan ba.

"Ana zarginsa da saka siyasa a al'amuransa. Yana saka siyasa kuma mun tabbatar da cewa ba za a mana adalci ba."

"Ba mu da matsala a kan bayanin da aka bukace mu mu yi da kuma bayyana gaban kwamitin wucin gadin. Amma matukar yana nan, babu wani bayani da za mu yi," yace.

Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa
Wawurar N40bn: Majalisar wakilai ta bada umarnin damko MD na NDDC da tawagarsa. Hoto daga TVC
Asali: Twitter

A wani labari na daban, jami'an 'yan sandan Najeriya sun tsinkayi gidan Joy Nunieh, tsohuwar mukaddashin manajan daraktan hukumar habaka yankin Neja Delta (NDDC), inda suka yi masa zobe.

Jami'an tsaron sun isa gidan ne da ke lamba 3, titin Owuru Creek, kusa da titin Herbert Macauley da ke tsohuwar GRA a Fatakwal, jihar Ribas a sa'o;in farko na ranar Alhamis.

Wannan ci gaba ya faru ne kafin isar Nunieh gaban kwamitin bincike na majalisar dattawa da ke Abuja inda za ta amsa tambayoyi a kan ayyukan NDDC.

A yayin da jaridar The Cable ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar Ribas, Omoni Nnamdi don tsokaci, ya bukaci a kira sa nan da mintuna 30.

Akpabio da Nunieh sun bayyana a gaban kwamitin rikon kwarya na majalisar dattawa, inda ake bincikarsa a kan badakalar wasu kudade har N40 biliyan wanda kwamitin rikon kwarya na hukumar suka lamushe.

A yayin sauraronsu, Akpabio ya ce bai san tsarin kudin kashewa na NDDC ba karkashin Nunieh saboda bata bashi bayanin da ya kamata.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel