Firimiya: A karon farko a tarihi, Jose Mourinho ya ci wasa a gidan Newcastle

Firimiya: A karon farko a tarihi, Jose Mourinho ya ci wasa a gidan Newcastle

- Harry Kane ya zura kwallaye biyu a wasan Tottenham da kungiyar Newcastle jiya

- Abin mamaki wannan ne karon farko da Jose Mourinho ya ci wasa a St James Park

- Tun shekarar 2004 da Mourinho ya ke aiki a Ingila, bai taba doke Newcastle a gida ba

Nasarar 3-1 da Tottenham ta samu a kan Kungiyar Newcastle ita ce ta farko da Jose Mourinho ya dandana a gasar Firimiya tun da ya fara horaswa a kasar Ingila.

Jose Mourinho ya doke Newcastle a gidanta na St James Park wannan karo bayan ya jarraba sa’arsa sau takwas bai dace ba a baya.

Kafin yanzu, Jose Mourinho ya gwabza da Newcastle da kungiyoyin Chelsea da Manchester United, amma duk bai taba samun maki uku a kan kungiyar ba.

“Su na wasa da kyau, sun san yadda ake kwallo, sun san yadda za su samu maki, su na da hadari ta wurare daban-dabam.” Mourinho game da Tottenham.

Da aka yi wa kocin magana game da wannan nasara mai tarihi da ya samu, ya bayyana cewa ba a jiya ne ya fara doke Newcasle a gida ba, ya yi hakan a lokacin da ya ke Chelsea.

KU KARANTA: Fernandes ya sake zama gwarzon wata a Ingila

Firimiya: A karon farko a tarihi, Jose Mourinho ya ci wasa a gidan Newcastle
Jose Mourinho Hoto: Tottenham
Asali: Getty Images

Jose Mourinho ya tabbatar da cewa ya taba cin wasanni biyu a filin St James Park a wasan karamin kofi. An yi haka na Nuwamban 2004, an kuma maimaita a Disamban 2006.

Saboda haka sai dai ace a ranar Laraba, 15 ga watan Yuli ne Mourinho ya fara samun sa’a a kan Newcastle a gidanta a gasar Firimiya.

Tsohon kocin na Real Madrid da Inter Milan ya yi amfani da wannan dama ta jiya, ya yabawa tsohon mai gidansa, Bobby Robson wanda ya daura shi a kan hanya.

Kocin ya yi aiki da Bobby Robson a matsayin tafinta a Porto da Sporting Lisbon kafin ya zama mataimakin mai horaswa, daga nan ne tauraruwarsa ta rika haskawa.

A wasan na jiya Kane ya ci kwallonsa na 100, Mourinho ya na ganin cewa ‘dan wasan zai iya kara cin wasu kwallaye 200. Ya kuma ce su na bukatar su ci wasannin su da su ka rage

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel