Bidiyon saurayi ya tsugunna tare da rungumo budurwa don neman aurenta a Kano ya janyo cece-kuce

Bidiyon saurayi ya tsugunna tare da rungumo budurwa don neman aurenta a Kano ya janyo cece-kuce

Bidiyon wani saurayi da ya tsuguna wa budurwarsa tare da sanya mata zobe a hannu don neman amincewarta a kan aurensa ya janyo cece-kuce.

Jama'a masu tarin yawa sun yi ta martani a jihar da kuma shafukan sada zumuntar zamani. Da dama suna cewa an kaucewa tsarin Musulunci ganin yadda budurwar ta fada jikin saurayin yayin da ya rungumota.

Ana cewa masoyan sun kwaikwayi al'adar Turawan yamma a maimakon bin ka'idar addinin Musulunci ko kuma al'adar bahaushe mai cike da kunya wurin neman aure.

Amma kuma, hukumar Hizbah ta jihar Kano ta ce babu shakka sai tayi martani a kan bidiyon da ya bulla.

Yayin da wasu jama'a da dama ke tofin Allah wadai ga masoyan, wasu sun ce basu ga laifinsu ba don kuwa zamani ne ya zo da yayi.

Babu aibu idan masoya sun bayyana tsananin soyayyar da suke wa junansu a bainar jama'a.

Bidiyon saurayi ya tsugunna tare da rungumo budurwa don neman aureta a Kano ya janyo cece-kuce
Bidiyon saurayi ya tsugunna tare da rungumo budurwa don neman aureta a Kano ya janyo cece-kuce. Hoto daga BBC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Magatakardan majalisar tarayya da wasu ma'aikata 150 sun yi murabus

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel