An yankewa wani baƙar fata hukuncin ɗauri na shekaru 48 bayan wata mata ta yi mummunan mafarki a kansa

An yankewa wani baƙar fata hukuncin ɗauri na shekaru 48 bayan wata mata ta yi mummunan mafarki a kansa

A kasar Amurka ne aka yankewa wani mutum baƙar fata hukuncin ɗauri na shekaru 48 bayan da wata mata ta yi mummunan mafarki a kansa na yin lalata da ita.

An zartar da hukuncin cin sarka har na tsawon shekaru 48 kan wannan mutun da aka zarge shida laifin cin zarafin wata mata baya ta yi ikirarcin cewa fuskarsa ce ta bayyana a mafarkinta.

Babu shakka a zahiri an yi wa matar fyade bayan fitowar daga wata mashaya inda ta yi tatul da giya tare da wasu maza uku.

Matar 'yar jihar Colorado ta shaidawa kotun cewa, Clarence Moses-El, shi ne ya ci zarafinta domin kuwa ta fuskarsa ta bayyana wani mummunan mafarki da ta yi.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, wannan lamari na ban tausayi kuma mai kama da almara, ya auku ne tun a shekarar 1988.

Abun al'ajabin ya auku ne sakamakon shiga cikin damuwa da matar ta yi da kuma kokarin tuna fuskar wanda ya ci zarafinta bayan ta yi mankas da giya, wanda ko wani ganin kirki da idanunta ba ta iyawa.

Clarence Moses-El
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Nation
Clarence Moses-El Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Nation
Asali: Twitter

Matar yayin bayar da shaida a gaban kotu ta bayyana cewa, Moses-El shi ne mutumin da ya ci zarafinta a yayin da take cikin halin maye domin kuwa ta iya hararo fuskarsa a wani mafarki da ta yi.

Moses-El ya yi iyaka bakin kokarinsa wajen kalubalantar wannan tuhuma da matar ta shimfida a kansa, sai dai babu yadda wajen hana kotu ta zartar da hukuncin kan laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Tun a wancan lokaci, rahotanni sun bayyana cewa, duk da hani da kotu tayi, jami'an hukumar 'yan sanda sun tarwatsa duk wasu hujjoji da dalilai da Moses-El zai iya yin amfani da su wajen kare kansa.

Sai dai da ya ke mai rabon gani badi sai ya gani, a shekarar 2013 ne daya daga cikin mutanen ukun da suka aikata wannan laifi, LC Jackson, ya aikewa da Moses-El wasika yayin da cin sarka a gidan Dan Kande.

Cikin wasikar da LC Jackson ya aikewa da Moses-El ta neman gafara, ya furta cewa ba bu shakka yana daya daga cikin mutanen da suka aikata laifin da ake zarginsa da shi.

KARANTA KUMA: Masu garkuwa a Kaduna na neman fansar N900m

A shekarar 2016 ne kotu ta wanke Moses-El daga duk wani zargi na laifukan da ake tuhumarsa.

A karshe dai, Moses-El ya shafe kusan shekaru 30 a kurkuku kan laifin da ba shi ya aikata ba.

Lauyan koli na jihar Colarado, Phil Wieser, ya shiga ya fita wajen tabbatar da cewa, an biya Moses-El diyyar dala miliyan 2 bayan ikirarin da LC Jackson ya yi.

Dokar jihar Colorado ta wanke mutum daga laifi, ta yi tanadin biyan dala 70,000 duk shekara ga mutumin da aka zartarwar da hukunci a bisa kure.

Musa-EL ya ce kudaden za su taimaka masa wajen dawo da martabar da ya rasa.

Kundin tarihi ya nuna cewa, Moses-El shi ne mutum na biyu da ya ribaci dokar wanke mutum daga laifi tare da karbar diyya wadda aka shata tun a shekarar 2013.

Yayin da aka tambaye shi furucin da zai yi a kan matar da ta zarge shi da fyade, "ya ce ba ya da ta cewa face yi mata fatan alheri, kuma yana mata fatan samun albarka a rayuwa."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel