Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta dubu 30 - NCDC
Bayan fiye da watanni hudu kenan da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 36 da kuma babban babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.
Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.
Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Cross River.
A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 11,670 sai kuma mutum 1,701 da suka warke, yayin da mutum 133 suka kwanta dama.
Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 30,249, sai kuma mutum 12,373 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 684 suka riga mu gidan gaskiya.

Asali: Twitter
Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 171,931 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Haka kuma alkaluman Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 17,192 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.
Da misalin karfe 11.53 na ranar Laraba da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 460 da cutar ta harba a fadin Najeriya.
KARANTA KUMA: Jami'in ɗan sanda ya harbe ɗan kabu-kabu saboda rashin sanya takunkumin rufe fuska a Imo
Sabbin mutane 460 da cutar ta harba cikin jihohi 21 sun kasance kamar haka: Lagos (150); Rivers (49); Oyo (43); Delta (38); Abuja (26); Anambra (20); Kano (20); Filato (18); Edo (14); Bayelsa (13); Enugu (13); Osun (12); Kwara (10); Borno (8); Ogun (7); Kaduna (6); Imo (4); Bauchi (3); Gombe (3); Neja (2); Adamawa (1).
Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu da mutum 2,348 yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku da mutum 1,573.
Ga jerin adadin mutanen da cutar ta harba cikin kowace daya daga cikin jihohi 36 na Najeriya da cutar ta bulla:
Legas - 11,670
Abuja - 2,348
Oyo - 1,573
Edo - 1,503
Delta - 1,323
Kano - 1,291
Ribas - 1,284
Ogun - 1,057
Kaduna - 889
Katsina - 628
Borno - 563
Ondo - 550
Gombe - 524
Bauchi - 519
Ebonyi - 503
Filato - 478
Enugu - 431
Abia - 400
Imo - 356
Jigawa - 318
Kwara - 307
Bayelsa - 282
Nasarawa - 234
Osun - 210
Sokoto - 153
Niger - 124
Benuwe - 121
Akwa Ibom - 112
Adamawa - 100
Anambra - 93
Kebbi - 86
Zamfara - 76
Yobe - 61
Ekiti - 45
Taraba - 27
Cross River - 5
Kogi - 5
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng