Osinbajo ya jagoranci gwamnoni 36 a zaman majalisar tattalin arziki

Osinbajo ya jagoranci gwamnoni 36 a zaman majalisar tattalin arziki

A ranar Alhamis, Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar tattalin arzikin kasa (NEC) a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Zaman majalisar wanda aka gudanar da shi a 'Yellow Room' da ke shiyyar ofishin mataimakin shugaban kasa, shi ne taro na biyu da aka yi ta hanyar kiyaye dokar nesa-nesa saboda annobar korona.

Ana gudanar da irin wannan zama ne sakamakon fafutikar da ake ci gaba da yi ta dakile yaduwar cutar korona a fadin kasar.

Ministar kudi, kasafi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ta halarci zaman yayin da gwamnonin jihohi 36 da ke fadin tarayya kasar suka halarta daga jihohinsu ta hanyar bidiyo.

Farfesa Yemi Osinbajo
Hoto daga; @MalaTujjani73
Farfesa Yemi Osinbajo Hoto daga; @MalaTujjani73
Asali: Twitter

Kamar yadda kundin tsarin mulkin ya tanada, mataimakin shugaban kasar shi ne shugaban majalisar tattalin arzikin kasa.

Ana gudanar da zaman wannan majalisa wata-wata domin tattaunawa kan batutuwan da suka shafi daidaito da shimifida tsare-tsare kan tattalin arzikin kasar a duk matakan daban-daban na gwamnati.

KARANTA KUMA: Harin 'yan bindiga: Mutane fiye da 5000 a ƙauyuka 8 sun tsere a Sakkwato

Majalisar tattalin arzikin kasar ta kunshi duk gwamnonin jihohi 36 da ke fadin tarayyar kasar, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Ministar Kudi da Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya.

Sauran 'yan majalisar sun hadar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, da duk wasu jami'ai da hukumomin gwamnati wanda nauyin da ya rataya a wuyansu ya tuke a kan tattalin arziki.

A bangare guda kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa, ganin irin rudanin da aka shiga, gwamnatin tarayya ta fito ta bayyana abin da ya ke faruwa game da tashin farashin mai a Najeriya.

Karamin ministan mai na kasa, Cif Timipre Sylva, a wani jawabi da ya sanya wa hannu a ranar Laraba, ya yi bayani dalla-dalla game da tsarin gwamnatin shugaba Buhari a kan harkar mai.

Ministan ya ce gwamnati ba za ta iya cigaba da batar da tiriliyoyin kudi duk shekara da sunan tallafin man fetur ba, musamman ganin yadda talakawa ba su amfana da tsarin sosai.

A cewar ministan tarayyar, gwamnati ta tashi daga jagorar masu shigo da mai a Najeriya. “Amma za a tallafawa ‘yan kasuwa su karbi ragamar shigo da kayan man.”

Timipre Sylva ya ke cewa: “Wannan yana nufin daga yanzu ‘yan kasuwa ne za su rika bayyana yadda kudin litar man fetur zai kasance.”

“Kamar dai yadda aka saba yi a kasashen da aka cigaba, gwamnati za ta cigaba da aikinta na sa ido, wajen ganin cewa ‘yan kasuwa ba su tsawwala farashi ba,” inji ministan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel