Doka ta 10: Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun gana a ranar Laraba

Doka ta 10: Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun gana a ranar Laraba

An sanar da cewa a yau Laraba, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya za su gana domin tattauna a kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi jihohinsu da kuma kasa baki daya.

Jigo cikin batutuwan da gwamnonin za su tattauna a kai shi ne kudirin sabuwar dokar nan da za ta ba wa majalisun dokoki da bangaren shari'a na jihohi 'yancin kai a fannin sha'anin kudi.

Cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar gwamnonin NGF, Abdulrazaque Bello-Barkindo, ya fitar a ranar Talata cikin birnin Abuja, ta nuna cewa a yau Laraba gwamnonin kasar za su gana da juna.

Wannan shi ne zama na 12 cikin jerin ganawa ta nesa-nesa da gwamnonin Najeriya su ka yi ta hanyar bidiyo tun bayan bullar cutar korona a kasar.

A ranar Juma’a, 22 ga watan Mayun 2020, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu a kan wannan doka da ta ba majalisar dokoki da hukumomi shari'a na jihohi damar cin gashin kansu.

Sabuwar dokar mai suna 'The Executive Order 10, 2020', za ta ba wa majalisar dokoki da bangaren shari'a na jihohi damar samun kudadensu kai-tsaye ba tare da ya bi ta hannun gwamnonin ba.

A karkashin wannan sabuwar doka, Buhari ya ba wa Ofishin Akanta Janar na kasa umarnin cire wa majalisar dokoki da bangaren shari’a kudaden su daga asusun duk wata jiha da ta ki bin wannan umarni.

Kungiyar Gwamnonin Najeriya; NGF
Hakkin mallakar hoto; NGF
Kungiyar Gwamnonin Najeriya; NGF Hakkin mallakar hoto; NGF
Asali: UGC

Domin gano ina suka dosa, Bello-Barkindo ya ce, ganawar gwamonin za ta fara ne da misalin karfe 2.00 na ranar Laraba, 8 ga watan Yuli.

Ya kuma yi bayanin cewa, dukkanin gwamnonin jihohi 36 na kasar za su halarta su na zaune a jihohinsu ta hanyar bidiyo.

Sauran batutuwan da gwamnonin za su tattauna a kai kamar yadda Barkindo ya bayyana sun hadar da matakan ceto tattalin arzikin kasar da ke kan gabar shiga cikin matsi.

KARANTA KUMA: Ta'addanci: An kama mata da miji da manyan bindigu a jihar Kebbi

Gwamnonin za su mayar da hankali musamman ga Hukumar zuba jari ta Najeriya, NSIA, domin tabbatar da tattalin arzikin kasar ya daidaita har zuwa lokacin da annobar korona za ta gushe.

Sai kuma batutuwan da suka shafi dawo wa da wasu jihohi biyar kudaden da suka kashe wajen aiwatar da wasu manyan ayyuka na gwamnatin tarayya.

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jerin jihohin sun hadar da Ribas, Bayelsa, Cross River, Ondo, da kuma Osun.

Barkindo ya ce gwamnonin za su yi bita kan harkallar cin hanci da rashawa a jihohinsu bisa la'akari da rahotannin da hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar.

A yayin taron, karamin ministan ma'adanan man fetur, Timipre Sylva, zai gabatar da jawabai kan batutuwan da suka shafi kamfanin sarrafa iskar gas na kasa (NLNG) da kuma shirin fadada kamfanin (NGEP).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel