Cutar korona ta hallaka mutum 654 a Najeriya - NCDC

Cutar korona ta hallaka mutum 654 a Najeriya - NCDC

Bayan fiye da watanni hudu da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 36 da kuma babban babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Litinin, 6 ga watan Yuli.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, babu jihar da ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, inda a baya bayan nan aka gano masu dauke da kwayoyin cutar karo na farko a jihar Cross River.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 11,367 sai kuma mutum 1,676 da suka warke, yayin da mutum 132 suka kwanta dama.

Kawo yanzu a duk fadin kasar, cutar ta harbi mutum 29,286, sai kuma mutum 11,828 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 654 da suka riga mu gidan gaskiya.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 152,952 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluman cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 16,804 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Da misalin karfe 11.34 na ranar Litinin da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 575 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

KARANTA KUMA: Zaben Gwamnan Ondo: PDP ta zabi Matawalle ya jagoranci kwamitin yakin neman zabe

Sabbin mutane 575 da cutar ta harba cikin jihohi 20 sun kasance kamar haka: Legas(123), Abuja(100), Delta(58), Edo(52), Ogun(42), Katsina(24), Bayelsa(23), Ribas(22), Borno(19), Filato(18), Ondo(18), Oyo(17), Kwara(15), Osun(13), Enugu(9), Nasarawa (7), Abia(6), Cross River(5), Kaduna(3), Ekiti(1).

Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu da mutum 2,281 yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku da mutum 1,530.

Ga jerin adadin mutanen da cutar ta hallaka cikin kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:

 1. Lagos - 132
 2. Abuja - 35
 3. Oyo - 19
 4. Edo - 50
 5. Delta - 25
 6. Kano - 52
 7. Ribas - 41
 8. Ogun - 21
 9. Kaduna - 12
 10. Katsina - 23
 11. Borno - 33
 12. Gombe - 21
 13. Bauchi - 12
 14. Ebonyi - 3
 15. Ondo - 20
 16. Filato - 14
 17. Abia - 3
 18. Enugu - 10
 19. Imo - 6
 20. Jigawa - 10
 21. Kwara - 9
 22. Bayelsa - 16
 23. Nasarawa - 8
 24. Osun - 7
 25. Sokoto - 16
 26. Neja - 7
 27. Akwa Ibom - 3
 28. Adamawa - 7
 29. Benue - 5
 30. Kebbi - 7
 31. Zamfara - 5
 32. Anambra - 9
 33. Yobe - 8
 34. Ekiti - 2
 35. Taraba - 0
 36. Kogi - 2
 37. Cross River - 1

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel