Abuja da jihohi 35 wanda cutar korona ta bulla a Najeriya
Bayan fiye da watanni hudu kenan da bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 da kuma babban babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.
Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Asabar, 4 ga watan Yuli.
Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.
A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 11,045 sai kuma mutum 1,653 da suka warke, yayin da mutum 132 suka kwanta dama.
Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 28,167, sai kuma mutum 11,462 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 634 suka riga mu gidan gaskiya.

Asali: Twitter
Rumbun tattaro bayanai na NCDC ya nuna cewa, an yi wa mutum 151,121 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Haka kuma alkaluma Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 16,071 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.
Da misalin karfe 11.35 na ranar Asabar da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 603 da cutar ta harba a fadin Najeriya.
KARANTA KUMA: Buɗe makarantu: Gwamnatin Tarayya za ta gana da gwamnatocin jihohi a ranar Talata
Sabbin mutane 603 da cutar ta harba cikin jihohi 19 sun kasance kamar haka: Legas(135), Edo(87), Abuja(73), Ribas(67), Delta(62), Ogun(47), Kaduna(20), Plateau (19), Osun(17), Ondo(16), Enugu(15), Oyo(15), Borno(13), Neja(6), Nasarawa(4), Kebbi(3), Kano(2), Sokoto(1), Abia(1).
Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu da mutum 2,153 yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku da mutum 1,466.
Ga jerin adadin mutanen da suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da cutar ta bulla:
Legas - 9,260
Abuja - 1,494
Oyo - 643
Edo - 588
Kano - 188
Delta - 795
Ribas - 396
Ogun - 317
Kaduna - 273
Katsina - 115
Borno - 58
Bauchi - 33
Gombe - 121
Ebonyi - 78
Filato - 190
Ondo - 275
Abia - 162
Enugu - 148
Imo - 296
Jigawa - 1
Kwara - 114
Bayelsa - 92
Nasarawa - 104
Osun - 99
Sakkwato - 12
Neja - 40
Akwa Ibom - 48
Benuwe - 59
Adamawa - 31
Kebbi - 19
Zamfara - 0
Anambra - 7
Yobe - 5
Ekiti - 1
Taraba - 9
Kogi - 0
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng