Matar Gwamnan Ondo ta kamu da cutar korona

Matar Gwamnan Ondo ta kamu da cutar korona

Mun samu rahoton cewa, kwayoyin cutar korona sun harbi matar gwamnan jihar Ondo, Misis Betty Akeredolu.

Hakan yana kunshe ne cikin tabbataccen rahoto da wani jami'in gwamnati a jihar ya tseguntawa manema labarai na jaridar Tribune a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuli.

Jami'in gwamnatin ya bayyana cewa, "kwanaki biyu da suka gabata ne aka dauki samfurin Uwargidan gwamnan da kuma daya daga cikin dogarawansa, kuma sakamakon da ya fito sa safiyar yau ya tabbatar da cewa suna dauke da kwayoyin cutar."

Sai dai ya bayyana cewa, "tuni uwargidan gwamnan ta killace kanta."

Gwamnan Ondo; Rotimi Akeredolu
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Premium Times
Gwamnan Ondo; Rotimi Akeredolu Hakkin mallakar hoto; Jaridar Premium Times
Asali: UGC

Ya kuma ce "a halin yanzu ana ci gaba da kirdadon sakamakon wasu daga cikin hadiman sadarwa na gwamna da wasu kwamishinoni da ke hulɗa da gwamnan jihar a kai a kai."

Ya ce, a baya bayan nan an gudanar da makamancin wannan gwaji kan mambobin majalisar dokokin jihar da kuma wasu sarakunan gargajiya wadanda suka shimfida goyon bayan kudirin gwamna Rotimi Akeredolu na neman wa'adi na biyu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, ajali ya katse hanzarin kwamishinan lafiya na jihar Ondo, Dakta Wahab Adegbenro.

Rahotanni daga fadar gwamnatin jihar sun nuna cewa kwamishanan ya yi gamo da ajali ne sakamakon cutar korona.

Mutuwar kwamishanan ya biyo bayan kamuwar gwamnan jihar da cutar ta Korona.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata 30 ga watan Yuni ta wani faifan bidiyo da ya wallafa a sahihin shafinsa na Twitter.

Akeredolu ya ce a lokacin da ya samu sakamakon gwajin, ba ya da alamomin cutar kuma tuni ya killace kansa.

KARANTA KUMA: 'Yan sandan Dubai sun danƙa Hushpuppi a hannun Hukumar FBI ta Amurka

Ya bukaci mutanen jiharsa su taya shi da adduo'i inda ya ce, "a halin yanzu ina bukatar adduoin samun sauki daga gare ku."

A cikin faifan bidiyon, Akeredolu ya ce, "Kwanaki baya na kamu da zazzabin cizon sauro kuma na warke. "

"A lokacin da muka je taron NEC na jamiyyar mu ta APC, takwarori na sun janyo hankali na."

"Na yi magana da daya daga cikinsu, ya jawo hankali na cewa bai dace a rika wasa da zazzabin cizon sauro ba a halin yanzu na annoba kuma ya ce na je a yi min gwajin cutar."

"Sakamakon gwajin ya fito a ranar 30 ga watan Yunin 22. Sakamakon ya nuna na kamu da cutar. Amma jiki na lafiya kalau ba ni da alamomin cutar."

"Bana jin wani canji a jiki na. Likitoci na sun ce in fara shan magungunan cutar sannan in killace kai na."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel