NSE ta bayar da kyautar N16m ga Dalibai 16 da suka ciri tuta a jarabawar JAMB ta 2020

NSE ta bayar da kyautar N16m ga Dalibai 16 da suka ciri tuta a jarabawar JAMB ta 2020

Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya NSE, ta bayar da kyautar naira miliyan 16 ga dalibai 16 da suka fi samun nasara a jarabawar bana ta Hukumar shirya jarabawar shiga jami'a da makarantu na gaba da sakandire wato JAMB.

Daliban da za su ci moriyar wannan kudade, sun nuna sha'awar ci gaba da karatuttukansu a fannin nazarin karatun injiniya a sashe daban-daban a jami'o'i mabanbanta.

Babagana Muhammad, shugaban NSE na kasa, shi ne ya bayyana hakan yayin wani taro na gabatar da daliban da suka yi zarra a ranar Talata cikin birnin Legas.

Ya ce makasudin wannan kyauta da kungiyar ta bai wa daliban shi ne janyo ra'ayin karin 'yan Najeriya su yi karatu a kan kwarewar aikin injiniya.

Kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito, daliban za su rika karbar naira dubu 200 duk shekara har na tsawon shekaru biyar masu zuwa da zarar sun samu nasarar shiga jami'a a bana.

NSE ta bayar da kyautar N16m ga Dalibai 16 da suka ciri tuta a jarabawar JAMB ta 2020
Hakkin mallakar hoto; Jaridar Premium Times
NSE ta bayar da kyautar N16m ga Dalibai 16 da suka ciri tuta a jarabawar JAMB ta 2020 Hakkin mallakar hoto; Jaridar Premium Times
Asali: UGC

A baya bayan nan ne hukumar JAMB ta fidda sunayen dalibai 13 da suka ciri tuta a jarabawar shiga jami'o'in ta bana.

Hukumar ta fidda sunayen daliban ne a yayin taron tsare-tsare da jadawalin da ta gudanar makonni biyu da suka gabata, daliban da suka ciri tuta a jarabawar bana sun sami maki tsakanin 352 da 365.

Biyu daga cikinsu da suka fito daga jihar Anambra, sun fi kowa samun nasara, inda suka samu maki 365 da kuma 363.

KARANTA KUMA: Asarar kudin haraji: Majalisa ta kira Ministar kudi, Emefiele, Magu da wasu kusoshin gwamnati

Wani dalibi da ya fito daga jihar Edo, ya biyo bayansu da maki 359, yayin da wasu dalibai biyu da suka fito daga jihar Ekiti, sun sami maki 358 da 356 a mataki na hudu da na biyar a jere da juna.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, wasu dalibai biyu da suka fito daga jihar Delta, sun samu maki 359 da 352.

Sauran jihohin da suka samun nasarar fito da zakakuran dalibai sun hadar Ekiti, Ondo, Akwa Ibom, Kwara, Oyo da kuma Ogun.

Daga cikin daliban 13 da suka fi yin fice a jarabawar ta bana, biyu sun samu maki 359, wasu biyun sun samu 355 yayin da wasu daliban hudu suka samu 352.

Hakan yana kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Fabian Benjamin ya fitar. Ga jerin sunayen daliban, jihohin da suka fito da kuma adadin makin da kowanensu ya samu:

1) Maduafokwa Egoagwuagwu Agnes -365

2) Nwobi Okwuchukwu David – 363

3) Ojuba Mezisashe Shalom – 359

3) Elikwu, Victor Chukwuemeka – 359

5) Adebola Oluwatobi Paul – 358

6) Gboyega Oluwatobiloba Enoch – 356

7) Ojo Samuel Oluwatobi – 355

7) Utulu, Jebose George – 355

9) Osom Akan Awesome – 353

10) Akakabota Fejiro Simeon – 352

10) Ogundele Favour Jesupemi – 352

10) Alatise Monsurah Bisola. – 352

10) Adelaja Oluwasemilore Daniel – 352

Dukkanin daliban sun nemi kwasa-kwasai a fannin nazarin karantun injiniya. Kama daga injiniyan masana'antu, gine-gine, kwamfuta, lantarki da sauransu.

Hudu suna neman shiga jami'ar Legas, biyu kuma jami'ar Covenant, jami'ar Obafemi Awolowo da kuma jami'ar Ilorin.

Dalibi daya kuma yana neman samun shiga jami'ar Jihar Kwara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel