'Yan takara 7 na jam'iyyar PDP na neman kujerar marigayi Sanata Osinowo

'Yan takara 7 na jam'iyyar PDP na neman kujerar marigayi Sanata Osinowo

An ruwaito cewa, akalla mambobi bakwai na jam'iyyar PDP ne suka nuna sha'awar tsayawa takara a zaben cike gurbi na mazabar kujerar shiyyar Legas ta Gabas a Majalisar Dattawa.

Haka kuma an tattaro cewa, wasu daga cikin mambobin jam'iyya mai mulki ta APC, sun nuna hankoronsu a kan kujerar.

Tsohon mai rike da wannan kujera, Marigayi Sanata Bayo Osinowo, ya mutu ne a watan da ya gabata bayan wata 'yar takaitacciyar rashin lafiya da aka ce tana da alaƙa da cutar korona.

Sanatan ya mutu ne a babban asibitin First Cardiologist dake Legas.

Marigayi Sanata Bayo Osinowo
Hakkin mallakar hoto; The Nation
Marigayi Sanata Bayo Osinowo Hakkin mallakar hoto; The Nation
Asali: UGC

Kamar yadda doka ta tanada, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta INEC, tana da kwanaki 90 na gudanar wani sabon zabe domin cike gurbin kujerar yayin da majalisar tarayya ta ayyana kujerar a matsayin fanko.

Manema labarai na jaridar The Punch sun samu nasarar tono wasu daga cikin mambobib jam'iyyar PDP da ke hankoron cike gurbin kujerar marigayi Sanata Osinowo.

Daga cikinsu akwai, tsohon dan takarar gwamnan jihar Legas a jam'iyyar ADP, Babatunde Gbadamosi; tsohuwar 'yar takarar kujerar sanatan shiyyar Legas ta Gabas a jam'iyyar PDP, Princess Abiodun Oyefusi.

Haka kuma akwai wani kwararren masani a kan sha'anin hulda da al'umma, Adedipe Shobajo da sauran.

Kakakin jam'iyyar PDP reshen jihar Legas, Taofik Ganiu, ya ce jam'iyyar za ta iya bakin kokarinta wajen tabbatar da tsayar da dan takara managarci da ya cancanci cin gajiyar marigayi Osinowo.

KARANTA KUMA: Annobar korona za ta kara tsananta talauci a tsakanin talakawa - Buhari

Legit.ng ta ruwaito cewa, majalisar dattawa ta ɗage zamanta na ranar Talata tare da yin shiru na minti daya domin yin jimamin mutuwar Sanata Bayo Osinowo.

Ajali ya katse hanzarin dan majalisar mai shekaru 64 a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, kwanaki hudu bayan dawowar majalisar daga hutun makonni biyu da ta yi.

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ovie Omo-Agege, wanda ya jagoranci zaman majalisar na ranar Talata a takaice, ya ɗage zamanta zuwa ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, kamar yadda aka saba a al'adar majalisar.

Jigo cikin dattawan majalisar, Yahaya Abdullahi, shi ne ya gabatar da kudirin ɗage zaman majalisar kuma aka aminta da shi cikin hazari babu ko jayayya.

Haka zalika, shugaban 'yan tsiraru watau marasa rinjaye na majalisar, Enyinnaya Abaraibe, shi ne ya yi gaggawar goyon bayan kudirin ɗage zaman majalisar da Sanata Abdullahi ya gabatar.

Sanata Osinowo ya mutu kwanaki hudu bayan dawowa daga hutun makonni biyu da majalisar dokoki ta tarayya ta yi a ranar 11 ga watan Yuni.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel