Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)

Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)

Sakamakon ayyukan dakarun sojin saman rundunar Operation Gama Aiki a kasuwan Ango da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja, dakarun sun datse ayyukan 'yan ta'addan yankin.

Sun yi aikin mai cike da nasara ne a daren 28 ga watan Yuni da sa'o'in farko na ranar 29 ga watan Yunin 2020.

Bayanan sirrin da dakarun suka samu na ayyukan 'yan bindigar ne yasa suka datsesu daga satar shanun da suka yi a yankin.

Kamar yadda ya dace, dakarun sun kai samamen ne ta jiragen yaki inda suka yi musayar wuta da 'yan bindigar, lamarin da yasa suka halaka wasu.

Kadan daga cikinsu sun tsere da raunika sakamakon harbin bindiga sannan an kame biyu daga ciki wadanda suka kasance 'yan kasar ketare.

A yayin jinjinawa rundunar Operation GAMA AIKI, shugaban dakarun sojin saman, Air Marshal Sadique Abubakar ya jinjinawa dakarun kan jajircewarsu da kwarewarsu.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da su bai wa dakarun hadin kai da goyon baya ta hanyar samar da bayanai masu muhimmanci don dawo da zaman lafiya da tsaro a dukkan yankuna.

Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)
Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna). Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Buratai ya koma Katsina, garinsu shugaba Buhari

Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)
Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna). Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna)
Operation Gama Aiki: Dakarun sojin sama sun damke barayin Shanu daga wata kasa (Hotuna). Hoto daga Defence HQ
Asali: Twitter

A wani labari na daban, an damke wani sojan Najeriya da ya yi wa shugaban rundunar sojin Najeriya da sauran shugabannin tsaro kaca-kaca a wani bidiyo.

A wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani, sojan mai mukamin Lance Corporal mai suna Martins, ya zargi shugaban rundunar sojin najeriya, Laftanal Janar Tukur Buratai da sauran shugabbanin kasar nan da rashin kokari.

Ya zargesu da nuna halin ko in kula a kan kashe-kashen da ke faruwa a sassan kasar nan. Ya ce 'yan bindiga da mayakan ta'addancin Boko Haram na cin karensu babu babbaka.

A bidiyon mai tsawo, Lance Corporal Martins ya ce shugabannin tsaron Najeriya sun gaza.

Ya kushe shugabannin tsaron Najeriya ballantana Buratai da shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, a kan yadda ake ci gaba da kashe-kashe.

Ya zargi cewa rundunar sojin ta bada umarnin tsare wasu dakarun wadanda suka bukaci makamai na zamani don yakar Boko Haram da sauran 'yan ta'adda a kasar nan.

Ya tabbatar da cewa akwai yuwuwar a kama shi ko kuma a kashesa saboda wannan bidiyon amma ya ce ya sadaukar da kansa ga kasarsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel