Motocin babban kwamandan soji sun buge dattijo a Katsina har lahira
Wani dattijo mai shekaru 75, Alhaji Salisu Ibrahim, ya rasa ransa a wani hatsarin mota da ya danganci ayarin motocin wani Kwamandan sojin kasa na Najeriya, Birgediya Janar Warrah Idris.
Hatsarin ya auku ne a ranar Litinin cikin jihar Katsina, yayin da ayarin motocin kwamandan sojin suka buge dattijon yana haye a kan baburinsa.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, Dattijon ya yi gamo da ajali ne bayan da ayarin motocin ke hanyarsu ta dawowa wajen daukan babban sojan bayan sun tsaya shan mai.
Mashaida wannan mummunan lamari sun bayyana cewa hatsarin ya auku ne daura da kwanar gidan Mani da ke kwaryar birnin Katsina.
An tattaro cewa, dattijon nan take ya mutu.

Asali: Twitter
Mukaddashin kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanal Sagir Musa, ya tabbatar da wannan lamari cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce tawagar dakarun soji wanda Birgediya Janar Idris ya jagoranta, ta ziyarci iyalan marigayi Ibrahim domin jajanta musu.
Sa dai a rahoton da sashen Hausa na jaridar Daily Trust ya ruwaito, ya bayyana cewa, ayarin motocin Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai ne suka buge dattijon.
KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya rage tsadar kudin aure a wuraren bauta - Minista
Dattijon mai inkiyar 'Yar Yara ya rasa ransa ne a yayin da ya ke kan hanyarsa ta kai katin gayyatar daurin auren diyarsa da za a yi ranar Juma'a mai zuwa.
Kamar yadda jaridar ta ruwaito, "wani ganau ya ce ya ga lokacin da ayarin motocin sojin da ke gudu suka buge tsohon a kan layin Yahaya Madaki da ke cikin birnin Katsina."
"Salisu Ibrahim ya rasa ransa ne sadda ya zo ketare hanya a kusa da Gidan Mani inda motocin suka dake shi kuma nan take ya riga mu gidan gaskiya."
"Motar da ke cikin ayarin da ta bige dattijon dai ba ta tsaya ba ko kuma direban ya nuna nadamar abin da ya faru", inji shi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng