An kara gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China

An kara gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China

Masana kimiyya sun kara bankado wata cuta sabuwa mai kamanceceniya da mura a China wacce suka ce akwai yuwuwar ta zama annobar duniya.

Cutar ta bayyana ne a kwanan nan kuma an gano tana tattare ne da aladu. Amma kuma masanan sun tabbatar da cewa mutane za su iya kamuwa.

Masanan sun damu da cewa akwai yuwuwar cutar ta rikide ta yadda za ta ci gaba da yaduwa daga mutum zuwa mutum har ta haddasa annoba a fadin duniya.

Duk da yake, ba wata babbar matsala bace ta gaggawa, amma sun tabbatar da cewa akwai dukkan alamun da ke nuna cewa cutar za ta iya sauyawa don shafar mutane, lamarin da yasa ake bukatar bibiyarta.

Sun ce sabuwar cuta ce kuma ba dole garkuwar jikin dan Adam ta iya karesu daga ita ba.

Masanan sun wallafa a mujallar Proceedings of National Academy of Sciences cewa ya dace a hanzarta bullo da matakai tsaurara na dakile yaduwar cutar a jikin aladu.

Kuma a dinga bibiyar masu aiki a masana'antun da ke ta'ammali da naman aladu.

An kara gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China
An kara gano wata cuta da ka iya zama annobar duniya a China. Hoto daga BBC
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: FG ta amince da bude makarantu, ta yanke karin hukunci 2

A wani labari na daban, akwai yuwuwar gwamnatin tarayya ta sake garkame wasu kananan hukumomi 18 a fadin kasar nan saboda su ke da kashi 60 na masu cutar korona a Najeriya.

Shugaban kwamitin yaki da annobar korona ta kasa, Boss Mustapha, ya bada wannan alamar a tattaunawar da yayi da jaridar The Punch tare da sauran manema labaran gidan gwamnati.

Ya zanta da su ne bayan jagorar da yayi wa sauran mambobin kwamitin don tattaunawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a ranar Litinin.

Mustapha, wanda shine sakataren gwamnatin tarayya, ya ce kananan hukumomin da al'amarin ya shafa za su shiga wani sabon tsarin kulle.

A yayin jaddada cewa kasar nan bata kai kololuwa ba dangane da annobar korona, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an kiyaye duk hanyoyin dakile cutar.

Ya kara da bada tsokaci a kan dalilin da yasa ba a cika mutuwa a kasar nan sakamakon cutar ba. Ya ce kashi 80 na wadanda suka harbu da cutar na da shekaru tsakanin 31 zuwa 40 ne wanda ya kwatanta da masu jini a jika.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel