Kakakin majalisar jihar Bauchi ya musanta karbar guraben aiki a shirin N-Power

Kakakin majalisar jihar Bauchi ya musanta karbar guraben aiki a shirin N-Power

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, ya yi tsokaci game da rahotanni da ke yaduwa a dandalan sada zumunta na cewa ya karbi gurabe a aikin shirin N-Power.

Honarabul Suleiman ya musanta zargin da ake yi na cewa, ministar Agaji da Ci gaban Al'umma, Sadiya Umar Farouk ta ba shi gurabe a aikin N-Power tare da shugaban majalisar dattawa da wasu 'yan majalisa na tarayya.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar da mai magana da yawunsa, Abdul Burrra ya fitar a ranar Lahadi yayin ganawa da manema labarai a birnin na Bauchin Yakubu.

Kakakin majalisar ya yi makakin yadda jaridar Sahara Reporters ta wallafa wannan rahoto ba tare da nuna kwarewar aiki ba na rashin tantance sahihancinsa da kuma tabbatar da ingancinsa.

Ya ce "wannan rahoto da jaridar Sahara Reporters ta wallafa almara ce kawai ta ba ta da wani asali ballantana tushe. Illa iyaka ta wallafa rahoton ne domin kawai ta yaudari masu karanta labaranta."

Ya yi kira ga al'umma da su yi watsi da duk wani rahoto ko bayanai masu danganta shi da karbar guraben aiki a shirin N-Power da ke gudana a yanzu.

Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman
Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Nation
Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Abubakar Suleiman Hakkin mallakar hoto; Jaridar The Nation
Asali: Twitter

A karshe kakakin majalisar ya kuma yabawa shugaban Muhammadu Buhari game da samar da shirin N-Power da gwamnatinsa ta yi.

Haka zalika, ya yi kira ga matasa a mazabarsa ta Ningi, da su gaggauta neman cin moriyar shirin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen rage rashin aikin yi a tsakanin su.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya musanta rade-radin da ke yaduwa na cewa an bai wa sanatoci gurabe a aikin N-Power da ake shirin daukan matasa a yanzu.

Sanata Lawan cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawunsa, Ola Awoniyi, ya misalta rahotannin a matsayin tatsuniya da shaci fadi.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Sanata Lawan ya nemi al'umma da su yi watsi da wannan rahotanni masu yaduwa da cewa an ba shi gurabe a aikin shirin N-Power da za a dauki matasa.

KARANTA KUMA: Na daɗe da sanin akwai yaudara tsakanin Tinubu da Buhari - Adebanjo

Kakakin shugaban majalisar yayin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar cikin birnin Abuja, ya ce wannan rahotanni da wasu kafofin yada labarai ke yadawa ba wani abu bane face kanzon kurege.

Sanarwar ta ce: "An jawo hankalin Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa zuwa wani rahoto da Sahara Reporters ta wallafa wanda ke nuna cewa Ma'aikatar Agaji da Ci gaban Al'umma, ta raba masa da sauran 'yan majalisar dokoki gurabe a aikin N-Power."

"Muna ba da shawara ga al'umma da su yi watsi da gaba daya wannan labaran karya da aka wallafa a kan Shugaban Majalisar Dattawa da sauran sanatoci."

"Ya kamata al'umma su sani cewa wannan rahotanni tatsuniyoyi ne kawai da ake yadawa domin bata sunan majalisar dattawa yayin da aka gaza bayar da tabbaci kan zargin da ake yi musu."

"Muna so mu jaddada cewa, Shugaban Majalisar Dattawa ko kuma ofishinsa ba ya da wata alaƙa ta kusa ko ta nesa da al'amuran daukan aikin shirin N-Power da ake gudanarwa a yanzu."

"Muna rokon kafofin yada labarai da su yi kokarin watsa rahotanni na gaskiya, ta hanyar riko da dabi'ar tabbatar da sahihanci wajen kafa hujja musamman kafin wallafa zargin da zai zama lahani ko kuma bata sunan jami'an gwamnati."

"A ƙarshe, muna sake bayar da tabbacin cewa, labarin da aka ambata yana da lahani kuma ya kamata a yi watsi da shi."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel