Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 24, 000 - NCDC

Mutanen da cutar korona ta harba a Najeriya sun zarta 24, 000 - NCDC

Bayan kusan watanni hudu kenan da bayan bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 na kasar da babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Asabar, 27 ga watan Yuni.

Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 10,026 sai kuma mutum 1,530 da suka warke, yayin da mutum 126 suka kwanta dama.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 24,077, sai kuma mutum 8,625 da aka sallam daga cibiyoyin killace masu cutar bayan sun samu waraka, yayin da mutum 558 suka riga mu gidan gaskiya.

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, an yi wa mutum 130,164 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

KARANTA KUMA: Abiola Ajimobi: Ganduje da iyalinsa sun je ta'aziyya wurin sirikansu

Haka kuma alkaluma Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 14,894 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Da misalin karfe 11.42 na ranar Asabar da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 779 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 779 da cutar ta harba cikin jihohin 22 sun kasance kamar haka: Lagos (285), Rivers(68), FCT(60), Edo(60), Enugu(56), Delta(47), Ebonyi(42), Oyo(41), Kaduna(19), Ogun(18), Ondo(16), Imo(12), Sokoto(11), Borno(9), Nasarawa(8), Abia(5), Gombe(5), Kebbi(5), Kano (4), Yobe (3), Ekiti(3), Osun(2).

Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu yayin da jihar Oyo ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da ta bulla:

 1. Lagos - 10,026
 2. Abuja - 1,736
 3. Oyo - 1,305
 4. Kano - 1,195
 5. Ribas - 1,050
 6. Edo - 933
 7. Delta - 828
 8. Ogun - 774
 9. Kaduna - 703
 10. Katsina - 528
 11. Bauchi - 497
 12. Gombe - 492
 13. Borno - 486
 14. Ebonyi - 327
 15. Jigawa - 317
 16. Abia - 302
 17. Filato - 298
 18. Imo - 290
 19. Enugu - 258
 20. Ondo - 232
 21. Kwara - 217
 22. Nasarawa - 206
 23. Bayelsa - 184
 24. Sokoto - 151
 25. Osun - 108
 26. Neja - 84
 27. Akwa Ibom - 83
 28. Zamfara - 76
 29. Kebbi - 76
 30. Adamawa - 73
 31. Anambra - 71
 32. Yobe - 59
 33. Benue - 47
 34. Ekiti - 43
 35. Taraba - 19
 36. Kogi - 3

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel