A karon farko: An amince da wani maganin korona a Turai
Hukumar kula da harkar lafiya ta nahiyar Turai ta aminta da magani mai suna Remdesivir domin amfani wajen magance cutar korona.
A shekarun da suka gabata an yi amfani da maganin wajen yakar cutar Ebola. A wannan lokacin kuwa ana ci gaba da gwajin maganin a wurin yakar korona.
A halin yanzu, hukumar kula dda harkar lafiya ta Turai ta aminta da fara amfani da Remdesivir a dukkan kasashen Turai.
Za a fara gwada maganin a kan yara masu shekaru 12 zuwa sama da ke fama da cutar nimoniya da wadanda suke bukatar na'urar taimakon numfashi.
Amma kuma kafin a fara amfani da maganin, ana jiran hukumar tarayyar Turai ta bada umarnin karshe.

Asali: UGC
KU KARANTA: Hotuna da bidiyon motocin alfarma da ke garejin Kaftin Ahmed Musa
A wani labari na daban, alkalumman hukumar yaki da cututtuka masu yaduwa na ranar Laraba, 24 ga watan Yuni, ya bayyana cewa mutum 649 sun sake kamuwa da cutar korona a Najeriya.
A jihar Legas an samu sabbin masu cutar 250, jihar Oyo an samu karin mutum 100 sai jihar Filato an samu karin mutum 40 da ke dauke da cutar.
A jihar Delta an samu karin mutum 40 sai jihar Abia inda aka samu karin mutum 28 yayin da aka samu karin mutum 27 a jihar Kaduna.
A jihar Ogun an samu karin mutum 22, jihar Edo an samu karin mutum 20, sai kuma jihar Akwa Ibom inda aka samu karin mutum 18.
A jihar Kwara an samu karin mutum 17, babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja an samu sabbin masu cutar har 17 yayin da jihar Enugu ta samu karin mutum 14.
A jihohin Neja da Adamawa an samu karin mutum goma sha uku-uku, sai jihar Bayelsa an samu sabbin mutum 7 da ke dauke da cutar.
Jihohin Osun da Bauchi sun samu karin mutum shida-shida sai jihar Anambra da ke da karin mutum hudu.
A jihar Gombe akwai karin mutum 3, yayin da jihar Sokoto ta samu karin mutum biyu. Jihohin Imo da Kano sun samu karin mutum daddaya.
Jimillar masu cutar a Najeriya ta kai 22,020 yayin da mutum 7613 aka sallamesu daga asibiti. Mutum 542 suka riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng