Hotunan miyagun al'adu 7 a fadin duniya masu matukar bada mamaki
Akwai wasu al'adu a fadin duniya da har yanzu aka kasa yadda su duk da muninsu. Al'adun sun zama wani bangare na mutane, hakan ne yasa wasu ke ganinsu daidai da hankali yayin da wasu ke ganinsu a sabanin hakan.
Ga wasu daga cikin al'adu bakwai a fadin duniya masu matukar bada mamaki.
1. Tafiyar gawa
Jama'ar Toraja da ke kasar Indonesia na yin wata al'ada ta sa gawa tayi tafiya kafin a birneta.
A wani kauye da ke tsaunikan kudancin Sulawesi, Indonesia, Shamans, matattu suna takawa bayan mutuwarsu.
Kamar yadda addininsu ya yarda, domin mamacin Toraja ya samu kwanciyar kabari mai kyau, dole ne a mayar da shi inda aka haifeshi sannan a birne.
Gawar na tashi da kanta ta taka har inda za a birneta.

Asali: Twitter
2. Al'adar El Colacho ta tsallake jarirai
Mazauna kasar Spain sun saba daukar wannan al'amarin mai matukar hadari mai suna El Colacho tun 1620.
A al'adar El Colacho, ana kwantar da jarirai inda ake tsallakesu don raba su da miyagun aljanu.
A wannan bikin, ana kwantar da jarirai a kan katifa a tituna sannan a dinga tsallakesu.

Asali: Twitter
3. Rayuwa da gawawwaki
Wannan salo ne na wasu kabilu da ke kasar Indonesia. Suna nade matattunsu a wasu irin akwatuna sannan su adana su a gidajensu. Sun yarda cewa wannan adanar na kammala ruhin masoyansu kafin a birnesu.
KU KARANTA: Magani a gonar yaro: Magungunan cutuka 7 da Zobo ke yi ga dan Adam
4.Sagale akwatunan gawa
Ana iya ganin akwatunan gawa da aka sagale a wurin kogin Yangtze da ke China. Wasu al'adu a kasar China suna birne gawawwakin mamatansu ne ta hanyar sagale akwatunan gawar.
Ana sagalesu ne a nisan kafa 33 zuwa 164, amma wasu na kai kafa 328 tsakaninsu da kasa. Suna sagale akwatunan gawa tun kafin shekarun 2000 da suka gabata.

Asali: Twitter
5. Wurgo jarirai daga sama
Wannan salon sananne ne ga jama'ar kauyen Solapur da ke Maharashtra a kasar India. Ana wurga jarirai daga nisan kafa 50.
Akwai jama'ar da ke jira a kasa inda za su rike zannuwa don saukar jinijirin. Suna cewa hakan na sa kananan yara su yi kyau, karko da kuma lafiya.

Asali: Twitter
6. Daukar mace a kan garwashi
A al'adar kasar China, miji na daukar amaryarsa a kan garwashi kafin ya shigar da ita gidansu a karon farko.
Sun yarda cewa hakan na sa mace ta samu sauki da rashin wahalar nakuda.
7. Makokin watan Muharram
A kowacce shekara a fadin duniya, mabiya akidar shia na makokin mutuwar Imam Hussain wanda ya yi shahada a hamadar Karbala a shekarar 680 AD.
A wannan ranar, suna fita da bulali hade da wukake sannan su dinga dukan kansu babu tsayawa. Wannan al'adar ta dade ana yinta kuma har yau ba a daina ba.

Asali: Twitter
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng