Ya zama tilas a tanadi wuraren killace masu cutar korona kafin a buɗe makarantu - Adamu Adamu

Ya zama tilas a tanadi wuraren killace masu cutar korona kafin a buɗe makarantu - Adamu Adamu

Gwamnatin Tarayya ta shata sharuɗa ga kafatanin makarantu da sauran cibiyoyin ilmantarwa a fadin tarayya da dole sai an cika kafin a sake buɗe su.

Sharuɗan da gwamnatin tarayya ta gindaya suna kunshe ne a cikin wata takarda mai shafi 36 wanda Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya gabatar wa Majalisar Dattawa.

Takardar wadda manema labarai na jaridar The Nation suka samu damar yin hange a kanta, an yi mata lakabi da ka'idodin sake buɗe makarantu da cibiyoyin ilimi bayan rufe su saboda annobar korona.

Mallam Adamu yayin gabatar da daftarin, ya sanar cewa wannan sharuɗa da aka shata su ne dabarun da za a aiwatar domin tabbatar da aminci da kuma ingancin sake buɗe makarantu.

Ministan ilimi - Adamu Adamu
Ministan ilimi - Adamu Adamu
Asali: Facebook

Ya ce ganin cewa annobar korona na iya kasancewa tare da mu har zuwa wani tsawon lokaci, sharuɗan da aka shata a yanzu su na jaddada muhimmancin inganta tsarin karantarwa daga nesa.

Ministan ya yi bayanin cewa, an shata wannan sabbin sharuɗa ne tare da hadin gwiwar kwararru daga ma'aikatun lafiya, zamantakewa da kuma na ilimi.

Ya ce kwararru sun jajirce wajen shimfida matakai da sharuɗan da za a kiyaye gabanin a samu amincin buɗe makarantu da sauran cibiyoyin karantarwa.

KARANTA KUMA: Coronavirus: Za a fara koyar da dalibai karatu ta gidajen rediyo talabijin a jihar Zamfara

Mafi muhimmancin cikin sharuɗan da aka gindaya, shi ne sai makarantu sun ƙirƙiri wuraren killace wadanda cutar korona ta harba na wucin gadi gabanin samun cancantar buɗewa.

Ya kuma zama wajibi ga duk makarantu su ƙirƙiri wata cibiyar kula da matakan dakile yaduwar cutar da za a rika kai dalibai, malamai da sauran ma'aikata yayin da suka kamu da rashin lafiya a makaranta.

Ya ci gaba da cewa, dole ne makarantu su tanadi isassun kayan aikin asibiti musamman na kare kai da kuma wuraren shan magani yadda ya dace.

Kazalika ministan ya ce za a tabbatar da kiyaye dokar sanya takunkumin rufe fuska, da kuma tanadar wadatattun wuraren wanke hannu a karkashin ruwa mai gudana ko kuma sunadarin wanke hannu (sanitizer).

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel