Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 20, 000 - NCDC

Adadin masu cutar korona a Najeriya ya zarta 20, 000 - NCDC

A yanzu kusan watanni hudu kenan bayan bullar cutar korona karo na farko a Najeriya, cutar mai toshe kafofin numfashi ta yadu a jihohi 35 na kasar da babban birnin kasar na Tarayya wato Abuja.

Wannan ya na kunshe cikin kididdigar alkaluman da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya NCDC ta fitar a daren ranar Litinin, 22 ga watan Yuni.

Har ila yau dai jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba a duk fadin kasar, sai da masu ruwa da tsaki sun ce rashin kayan aiki da karancin ma'aikatan lafiya ya yi tasiri a kan lamarin.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba babu sassauci, har yanzu jihar Legas ce ke jan ragama ta yawan masu cutar inda ta harbi mutum 8,864, sai kuma mutum 1,448 da suka warke, yayin da mutum 126 suka kwanta dama.

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 20,919, sai kuma mutum 7,109 da suka samu waraka, yayin da mutum 525 suka riga mu gidan gaskiya.

Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Shugaban NCDC; Chikwe Ihekweazu
Asali: Twitter

Taskar bayanai ta NCDC ta nuna cewa, an yi wa mutum 117,569 gwajin cutar a duk fadin kasar tun bayan bullarta karo na farko a ranar 27 ga watan Fabrairu.

Haka kuma alkaluma Cibiyar dakile cututtuka ta kasar sun nuna cewa, mutum 13,285 ne suka rage masu dauke da kwayoyin cutar.

Da misalin karfe 11.14 na ranar Litinin da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 675 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 436 da cutar ta harba cikin jihohin 19 sun kasance kamar haka: Lagos(288), Oyo(76), Rivers(56), Delta(31), Ebonyi(30), Gombe(28), Ondo(20), Kaduna(20), Kwara(20), Ogun(17), FCT(16), Edo(13), Abia(10), Nasarawa(9), Imo(9),Bayelsa(8), Borno(8), Katsina(8), Sokoto(3), Bauchi(3), Plateau(2).

Baya ga jihar Legas da ta ke kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, birnin Abuja ya biyo bayanta a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu a mataki na uku.

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da ta bulla:

 1. Lagos - 8,864
 2. FCT - 1,583
 3. Kano - 1,190
 4. Oyo - 988
 5. Rivers - 930
 6. Edo - 797
 7. Ogun - 663
 8. Kaduna - 600
 9. Delta - 532
 10. Gombe - 479
 11. Borno - 476
 12. Bauchi - 467
 13. Katsina - 434
 14. Jigawa - 317
 15. Ebonyi - 264
 16. Plateau - 253
 17. Imo - 243
 18. Abia - 232
 19. Kwara - 200
 20. Nasarawa - 193
 21. Bayelsa - 177
 22. Ondo - 154
 23. Enugu - 144
 24. Sokoto - 138
 25. Zamfara - 76
 26. Kebbi - 67
 27. Anambra - 66
 28. Niger - 66
 29. Akwa Ibom - 65
 30. Osun - 60
 31. Yobe - 56
 32. Adamawa - 45
 33. Benue - 44
 34. Ekiti - 35
 35. Taraba - 18
 36. Kogi - 3

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel