Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha guba

Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha guba

Wani mutum dan Najeriya me zama a Victory Park Estate da ke Lekki a jihar Legas, ya kashe kansa bayan ya sokawa matarsa wuka har lahira.

Bala Elkana, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ga The Cable Lifestyle a ranar Litinin, ya ce an adana gawawwakin mamatan a ranar Lahadi.

Ya ce a lokacin da 'yan sandan suka isa wurin da abun ya faru, kumfa ce ke fita daga bakin mutumin, lamarin da ke nuna cewa guba ya sha.

Matarsa kuwa na kwance a cikin jininta.

Elkana ya ce an dauke wukar wacce ake tunanin an yi amfani da ita wurin kashe matar tare da kwalaben Sniper, wanda ake tsammanin ya yi amfani da shi wurin kashe kansa.

Kakakin ya kara da cewa, yayin da ake binciken yadda lamarin ya auku, ana tsammanin mutumin ya soka wa matarsa wuka sannan ya kashe kansa daga baya.

Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha guba
Mutuwar kasko: Miji ya soka wa matarsa wuka sannan ya sha guba. Hoto daga The Cable Lifestyle
Asali: Twitter

KU KARANTA: Tsaro: Buratai ya yi taron gaggawa da kwamandojinsa (Hotuna)

"Zan iya tabbatar muku da aukuwar lamarin. Mun mika gawawwakin asibiti don gwajin abinda ya kasheta. Mun ganta a cikin jini," Elkana ya sanar da The Cable Lifestyle.

"Wukar yanka ce aka samu a wurin tare da kwalbar sniper biyu wacce ake tsammanin ya sha domin kumfa ce ke fita daga bakinsa.

"Likitoci za su gano silar mutuwarsu duk da hasashe a yanzu na nuna cewa ya kasheta ne sannan ya kashe kansa. Ana ci gaba da bincike," yace.

Amma kuma har yanzu ba a gane abinda ya kai mutumin da yin wannan aika-aikar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel