Ministan Shari'a ya ba da sunayen mutum 3 da za su maye kujerar Magu

Ministan Shari'a ya ba da sunayen mutum 3 da za su maye kujerar Magu

Ministan Shari'a Abubakar Malami, ya ba da sunayen mutane uku da za su iya maye gurbin Ibrahim Magu, mukaddashin Shugaban Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki ta'annati, EFCC.

Malami wanda kuma shi ne Lauyan Koli na Najeriya, ya ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara a kan mutane uku da zai iya zaba wajen maye kujerar Ibrahim Magu.

Sunayen mutum uku da Ministan ya aikewa da Buhari su cikin wata wasika suna hadar da Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan sanda, DIG Muhammad Sani Usman mai ritaya.

Sauran biyun su ne; Kwamishinan 'Yan sanda na Abuja, Bala Ciroma wanda shi ne shugaban kula da sashen gudanarwa na EFCC, da kuma wani Tsohon Mataimakin Sufeton 'Yan Sanda AIG daga jihar Kebbi.

Ministan Shari'a Abubakar Malami da Shugaba Buhari
Ministan Shari'a Abubakar Malami da Shugaba Buhari
Asali: Facebook

Gabanin yanzu, Malami ya taba neman Buhari ya maye gurbin Magu da DIG Usman ko kuma Ms Diseye Nsirim-Poweigba, wata tsohuwar kwamishinan 'yan sanda a jihar Neja.

Ministan ya ba da shawarar a zabi daya daga cikin mutane biyun yayin da tsohuwar majalisar dattawa ta ki amincewa da nadin Magu a matsayin shugaban Hukumar ta EFCC.

Sai dai wata majiya kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ta bayyana cewa, a yanzu shugaba Buhari bai da ra'ayin daukar Ms Diseye a matsayin wadda za ta gaji kujerar Magu.

KARANTA KUMA: Hukumar JAMB ta bayyana sunayen dalibai 13 da suka fi yin fice a jarabawar bana

Ana iya tuna cewa, a makon jiya ne dai Ministan Shari'a ya aikewa da shugaban kasa Buhari wasikar kar ta kwana kan mukaddashin shugaban Hukumarr EFCC wato Magu.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Malami ya bukaci shugaban kasa Buhari ya tsige shugaban hukumar hana almundahanan daga mukaminsa bisa wasu zarge-zargen rashawa da akalla sun kai 20.

Daga cikin laifukan da Ministan ya ke zargin Magu ya aikata sun hadar da karkatar da akalar dukiyar da aka kwato daga hannun wadanda suka yi sama da fadin kudaden gwamnati.

Haka kuma Ministan yana tuhumar Magu da rashin yi masa biyayya duk da Hukumar EFCC tana karkashin Ma'aikatarsa ta Shari'a.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel