Yanzu-yanzu: Mutum 436 sun harbu da korona, jimilla ta haura 20,000

Yanzu-yanzu: Mutum 436 sun harbu da korona, jimilla ta haura 20,000

Alkalumman hukumar yadki da cututtuka masu yaduwa (NCDC) na ranar 21 ga watan Yunin 2020 ya nuna cewa mutum 436 a Najeriya sun sake kamuwa da cutar korona.

Hukumar ta bayyana cewa an samu sabbin masu cutar korona 169 a jihar Legas yayin da jihar Oyo aka samu sabbin masu cutar har 52.

Jihar Imo da ke kudancin Najeriya ta samu karin mutum 29, jihar Kaduna ta samu sabbin mutum 28 sai jihar Ogun ta samu karin mutum 23.

Babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta samu karin mutum 18, jihar Enugu ta samu karin mutum 18 yayin da jihar Bauchi ta samu karin mutum 17.

Jihar Bayelsa ta samu sabbin masu cutar har 14 yayin da jihar Ribas ta samu karin mutum 8.

Jihohin Osun da Kano sun samu karin mutum shida-shida, sai jihohin Edo da Benue sun samu sabbin masu cutar har biyar-biyar.

Jihar Adamawa ta samu karin mutum uku, jihar Borno mutum biyu sai jihohin Abia da Ekiti da ke da daddaya.

Jimillar masu cutar a fadin Najeriya sun kai 20,244 yayin da mutum 6,879 suka warke daga jinyar muguwar cutar.

Mutum 518 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon muguwar cutar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel