Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aikin sai baba-ta-gani da suka shiga

Yanzu Yanzu: Likitoci sun janye yajin aikin sai baba-ta-gani da suka shiga

Kungiyar manyan Likitoin Najeriya National Association of Resident Doctors (NARD), ta yanke shawarar janye yajin aikin sai baba-ta gani da ta tsunduma.

Hakan yana kunshe cikin sanarwa da shugaban kungiyar, Dr Aliyu Sokomba, Babbar Sakatariya, Dr Bilqis Muhammad da kuma Mai magana da yawun kungiyar, Dr Stanley Egbogu, suka fitar.

Cikin sanarwar da manyan kushoshin kungiyar suka sanya wa hannu, sun ce janye yajin aikin da suka yi zai fara tasiri ne daga ranar Litinin, 22 ga watan Yuni.

Fusattatun likitocin a ranar Litinin ta makon da ya gabata sun tsunduma cikin yajin aiki na sai baba-ta-gani bayan karewar wa'adin makonni biyu da suka bai wa gwamnatin tarayya.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, kungiyar Likitocin ta shiga yajin aikin ne bayan da gwamnatin tarayya ta gaza biyan bukatun da ta nema a wurinta.

Da ta ke bayyana dalilin shawarar da ta yanke a yanzu, kungiyar likitocin ta ce ta janye yajin aikin ne domin bai wa gwamnatin kasar sararin yin nazari a kan bukatun da ta shigar.

Kungiyar Likitocin bayan sun tashi baram-baram a zaman masalaha da suka yi da gwamnatin tarayya a makon da ya gabata
Kungiyar Likitocin bayan sun tashi baram-baram a zaman masalaha da suka yi da gwamnatin tarayya a makon da ya gabata
Asali: Twitter

Hakan ya biyo bayan rokon da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi da sauran masu ruwa da tsaki suka yi.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta tsoma baki cikin rashin jituwar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da kungiyar Manyan Likitoci da har ta kai ga shigarsu yajin aiki.

Shugaban sashen hulda da al'umma na kungiyar gwamnonin, Abdulrazaque Bello-Barkindo, shi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

KARANTA KUMA: An sake kashe mutum 10 a wani sabon hari da aka kai jihar Zamfara

A sanarwar da Barkindo ya fitar, ya ce kungiyar gwamnonin ta gana da fusatattun Likitocin, sun kuma yanke shawarar sanya amincinsu a hannunta domin sulhunta lamarin.

Likitocin yayin bayyana fushinsu ga kungiyar gwamnonin, sun kuma ba da tabbacin za su janye aikin da suka shiga da zarar an cimma wata matsaya mai karfi.

An ruwaito cewa, dukkanin manyan kungiyar likitocin ta NARD sun hallara a sakateriyar NGF inda suka gana da shugaban NGF, Kayode Fayemi, wanda ya kasance gwamnan jihar Ekiti.

Daga bisani kungiyar likitocin a gaban Darakta Janar na NGF, Asinshana Bayo Okauru, sun kuma gana da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, inda shi ma suka bayyana masa fushinsu.

Wannan shi ne karo na farko da kungiyar likitocin ta kai kukanta har gaban kungiyar gwamnonin kamar yadda jaridar The Nation ta wallafa.

Gwamna Fayemi ya yaba ma likitocin kan yadda suka ci gaba da zama a kasarsu domin yin hidima duk da tarin alheri da kuma tayin da suke samu daga kasashen waje.

Sai dai Gwamnan ya tunatar da su cewa tserewa daga kasarsu ba tare da yi mata hidima ba zai zama butulci ga gwamnatin kasar da ta yi ruwa da tsaki wajen ganin sun kware a kan aikinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel