Yaki da COVID-19: Dole Najeriya ta yi watsi da siyasar bangare - Dr. Matazu

Yaki da COVID-19: Dole Najeriya ta yi watsi da siyasar bangare - Dr. Matazu

Fitaccen malami kuma dan siyasa, Dr. Garba Shehu Matazu, ya jaddada bukatar watsi da siyasar bangare wurin yaki da kalubalen annobar Coronavirus a kasar nan.

A halin yanzu, cutar ta harba sama da mutum 17,000 tare da zama silar mutuwar mutane masu tarin yawa.

Amma kuma, dan siyasar da yayi wakilci sau uku a majalisar wakilan kasar nan ya ce, sakamakon aikin sadaukar da kai da likitocin kasar nan keyi, an samu mutane masu tarin yawa da suka warke daga muguwar cutar.

Dr. Matazu ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a Abuja game da cutar. Ya ce akwai yuwuwar Najeriya ta dakile cutar da yaduwar, da ta rufe iyakokinta da wuri kafin karshen watan Maris.

Ya tunatar da lokacin da tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP a 2019, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta saka tsauraran matakai a kan jiragen da ke sauka da tashi a kasar nan tun bayan bullar cutar a karon farko.

Ya ce: "Domin cire shakku, Atiku Abubakar ya yi kira ga gwamnatin kasar nan a watan Fabrairu a kan cewa lokaci yayi da za a tsayar da sauka da tashin jiragen sama na wucin-gadi daga duk wata kasa da cutar tayi kamari.

"Akwai matukar amfani idan aka tsare rayuka fiye da tattalin arziki.

"Akwai bukatar samar da na'urorin binciken lafiya a filayen jiragen kasarmu."

Yaki da COVID-19: Dole Najeriya ta yi watsi da siyasar bangare - Dr. Matazu
Yaki da COVID-19: Dole Najeriya ta yi watsi da siyasar bangare - Dr. Matazu. Hoto daga Bashir Ibrahim Matazu
Asali: Facebook

KU KARANTA: Iyakar Zamfara da Katsina: Dakarun sojin sama sun ragargaza sansanin 'yan ta'adda

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Dr. Matazu ya ce tun a ranakun karshen makon da Gwamna Fayemi ya sanar da rufe hanyoyin shigowa kasar nan, yawan masu cutar ba zai daina hauhawa ba har zuwa watan Yuni da Yuli sakamakon watsi da aka yi da kiran da Atiku Abubakar yayi.

Mamban a majalisar amintattun jam'iyyar PDP mai wakiltar jihar Katsina, ya ce da an rungumi shawarar Wazirin Adamawa, da an tseratar da rayukan 'yan Najeriya masu tarin yawa.

Dr. Matazu ya sake jaddada cewa, kasar nan na bukatar hadin kai ne don shawo kan wannan matsalar. Ya yi kira ga gwamnati da tayi watsi da siyasar bangare a yayin da take yakar muguwar cutar nan da ta zama ruwan dare.

"Duk wata shawarar da aka bada, kamata yayi a duba amfaninta. Akwai bukatar a hada kai ba tare da an duba bangare ko ra'ayin siyasa ba.

"Za a iya nasara ne idan aka yi matukar kokari kuma gwamnatin tarayya ta hada kai da gwamnatocin jihohi," cewar fitaccen dan siyasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel