Kaduna da Kebbi da Zamfara ba su samu Sakatarorin dindindin ba

Kaduna da Kebbi da Zamfara ba su samu Sakatarorin dindindin ba

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin sabbin sakatarorin dindindin guda 12 a ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Sai dai cikin jerin sabbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya da shugaba Buhari ya bayar da lamuni, akwai wasu jihohi hudu da ba su samu gurbi ba a nadin da aka yi.

A sanarwar da Ofishin shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya (HoSF), Dr Folasade Yemi-Esan ya fitar, bai nuna sunayen sabbin manyan sakatarorin gwamnatin tarayya daga jihohin hudu ba.

Jihohin hudu da ba su samu gurbi ba a mukaman manyan sakatarorin gwamnatin tarayya 12 da shugaban kasar ya nada sun hadar da Ribas da Zamfara da Kaduna da kuma Kebbi.

Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya: Dr Folasade Yemi-Esan
Shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya: Dr Folasade Yemi-Esan
Asali: UGC

A kan shafinsa na dandalin sada zumunta, hadimin shugaban kasa Bashir Ahmed, ya sanya takardar da ta fito daga ofishin shugabar ma'aikatan mai dauke da sunayen sabbin sakatarorin 12.

A baya dai ofishin ya nuna cewa akwai gurabu 16 na sabbin manyan sakatarorin gwamnatin Tarayya da za a nada daga cikin daraktoci 41 da suka yi jarabawa a makonnin baya.

Sai dai jerin sunayen da aka fitar ranar Talata bai bayyana dalilin rashin sanya sunayen wakilan jihohin Zamfara, Kebbi, Kaduna da kuma Ribas ba.

A sanarwar da direktan watsa labarai na ofishin shugabar ma'aikatan tarayya, Mrs Olawunmi Ogunmosunle ta fitar, za a sanar da ranar da za a rantsar da sabbin sakatarorin nan gaba.

Ga sunayen sabbin sakatarorin da jihohin da suka fito kamar haka;

1. Akinlade Oluwatoyin, Kogi

2. Alkali Bashir Nura, Kano

3. Anyanwutaku Adaora lfeoma, Anambra

4. Ardo Babayo Kumo, Gombe

5. Belgore Shuaib Mohammad Lomido, Kwara

6. Ekpa Anthonia Akpabio, Cross River

7. Hussaini Babangida, Jigawa

8. Mahmuda Mamman, Yobe

9. Meribole Emmanuel Chukwuemeka, Abia

10. Mohammed Aliyu Ganda, Sokoto

11. Tarfa Yerima Peter Adamawa da

12. Udoh Moniloja Omokunmi, Oyo.

Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta fitar da jerin Daraktoci 41 da suka samu nasarar wucewa zagayen karshe na jarabawar ɗaga likafarsu zuwa matakin sakatarorin dindindin.

Darakatocin 41 sun fito ne daga cikin mutum 91 da suka zana jarabawar tantance ƙwarewarsu ta Fasahar Sadarwar Zamani a ranar Alhamis cikin birnin Abuja.

Manema labarai a ranar Asabar sun samu kwafin wasikar da ta bayyana jerin manyan ma'aikatan 41 da suka samu nasarar wucewa zagayen karshe na jarabawar ɗaga likafarsu.

Wasikar tana dauke da kwanan watan ranar 6 ga Yunin 2020 wadda darekan ofishin kula da sakatarorin dindidin, I.A Mairiga, ya sanya wa hannu a madadin shugabar ma'aikata.

Mairiga ya lura cewa, a yanzu Daraktoci 41 da suka samu nasara za su zauna zagayen karshen na jarabawar ɗaga likafarsu, wadda za ta kasance zantawar baki, a ranar Litinin, 8 ga watan Yuni.

A wasikar mai lamba HCSF/CMO/AOD/012/VOL. VI/42, ana gayyatar Daraktocin 41 su hallara a dakin taro na Olesugun Obasanjo da ke harabar Sakateriyar Tarayya da misalin karfe 8.00 na safiyar Litinin.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, 16 daga cikin Daraktocin 41 ne kadai ake sa ran za su zama sakatarorin dindindin kamar yadda wasikar ta bayyana.

Tun a sanawar da Yemi-Esan ta gabatar a ranar 23 ga watan Maris, ta nuna cewa za a gudanar da jarrabawar nada sabbin sakatarorin dindindin 16 a wasu ma'aikatu na gwamnatin tarayya.

Ta ce Daraktocin 14 da suka yi nasara za su maye gurbin sakatarorin dindindin da za su yi ritaya a bana, yayin da sauran biyun kuma za su maye guraben da babu kowa a kujerunsu.

Cikin sanarwar, sakatarorin dindindin da za su yi ritaya a bana sun fito ne daga jihohin Kebbi, Kwara, Abia, Anambra, Cross River, Kaduna, Kano, Oyo, Rivers, Sokoto, Adamawa, Yobe, Gombe da Jigawa.

Zamfara da Kogi su ne sauran jihohin biyu da ba su da sakatororin dindindin a kowane daya daga cikin ma'aikatun gwamnatin tarayya.

Yemi-Esan ta sake nanata cewa, ɗaga likafar za ta takaita ne kadai a kan ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka kai matsayin darakta a matakin albashi na 17 kafin 1 ga watan Janairun 2018.

Haka kuma zana jarabawar ɗaga likafar za ta kasance kan ma'aikatan da suka sabunta bayanan su a kan tsarin biyan albashin bai-daya (IPPIS) da gwamnatin tarayyar kasar ta fito da shi.

Ta kara da cewa domin cancanta, irin wadannan jami'ai dole ne su fito daga wasu jihohin kasar nan kuma bai kamata su yi ritaya ba daga yanzu zuwa ranar 31 ga watan Dasumba na 2021.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel