Yanzu Yanzu: Gwamna Obaseki ya fice daga jam'iyyar APC

Yanzu Yanzu: Gwamna Obaseki ya fice daga jam'iyyar APC

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya yanke shawarar ficewa daga jam'iyya mai ci ta APC bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Obaseki ya bayar da shaidar hakan yayin ganawa da manema labarai na fadar shugaban a ranar Talata, 16 ga watan Yuni.

Gwamnan ya yi furucin hakan ne a kan hanyarsa ta fita daga da fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja.

Yayin zantawarsa da manema labarai a fadar, Obaseki ya ce zai nemi takarar wa'adi na biyu a wata jam'iyar ta daban.

Biyo bayan hana shi takara da uwar jam'iyar APC ta yi, tun a ranar Lahadin da ta gabata ne dai Obaseki ya bayyana cewa, zai yanke shawarar matakinsa na gaba bayan ya gana da Buhari.

Shugaban kwamitin tantance 'yan takara na jam'iyyar APC, Jonathan Ayuba, shi ne ya bayar da sanarwar haramtawa Gwamna Obaseki tsayawa takara tun gabanin zaben fidda gwani.

Gwamna Obaseki da Buhari
Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Gwamna Obaseki da Buhari Hakkin mallakar hoto: Fadar shugaban kasa
Asali: Twitter

Ayuba ya bayyana cewa an haramta wa Obaseki tsayawa takarar ne sakamakon matsalar da ake gano akwai tattare da takardun makaranta na gwamnan.

Akwai yiwuwar babu inda gwamnan zai jarraba sa'arsa ta tsayawa takarar gwamnan sai a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP bayan ya cika bujensa da iska daga jam'iyyar APC.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, daman tuni dai jam'iyyar PDP ta fara zawarcin gwamnan yayin da uwar jam'iyyar APC ta huro masa wuta.

Haka zalika, an kwana biyu ba a 'yar ga maciji tsakanin Gwamna Obaseki da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Kwamared Adams Oshiomhole, wanda ya goyi bayansa a shekarra 2016.

KARANTA KUMA: Covid-19: Mun samu gudunmuwar N1.69bn tsakanin watan Afrilu da Mayu - Gwamnatin Tarayya

Lamarin da ya sanya tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya shawarci Gwamna Obaseki a kan komawa jam'iyyar PDP, inda ya kudiri aniyar zai shige masa gaba.

Legit.ng ta ruwaito cewa, a karshen makon da ya gabata ne Gwamna Obaseki ya gana da takwarorinsa na jihar Rivers, Nyesom Wike da kuma na Akwa Ibom, Emmanuel Udom.

Dukkanin gwamnonin biyu sun kasance 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.

A halin yanzu ana ganin cewa, Oshiomhole ya na goyon bayan Osagie Ize-Iaymu, wanda tuni aka share masa hanyar fitowa takarar gwamnan na jihar Edo a karkashin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel