Jihohi 35 da cutar korona ta bulla a Najeriya - NCDC

Jihohi 35 da cutar korona ta bulla a Najeriya - NCDC

- A yanzu cutar korona ta bulla a jihohi 35 na Najeriya da kuma babban birnin kasar na Tarayya

- Jihar Legas ce ke jan ragama inda ta harbi mutum 7,103, mutum 1,137 suka warke sai kuma mutum 82 da suka kwanta dama

- Jihar Cross River ce kadai ba a samu bullar cutar ba cikin dukkanin jihohin Najeriya

- A halin yanzu cutar ta harbi mutum 18,085, sai kuma mutum 5,220 da suka samu waraka, yayin da mutum 420 suka riga mu gidan gaskiya

Ya zuwa yanzu dai an samu bullar cutar korona a jihohi 36 na Najeriya ciki har da birnin tarayya kamar yadda kididdigar hukumar dakile cututtuka masu yaduwa a kasar NCDC ta tabbatar.

Tabbas mahukuntan lafiya na ci gaba fadi-tashi ba dare ba rana domin dakile yaduwar cutar korona a Najeriya, sai dai fa lamarin ya ci tura domin kuwa cutar na ci gaba da bazuwa tamkar wutar daji.

Taskar bayanai ta NCDC a ranar Lahadi, 14 ga watan Yunin 2020, ta ce cutar korona ta harbi mutane 18,085 a duk fadin kasar.

Haka kuma alkaluman sun nuna cewa an sallami mutum 5,220 daga cibiyoyin killace masu cutar bayan da suka warke.

Jadawalin NCDC ya tabbatar da cewa ya zuwa yanzu dai cutar corona ta hallaka mutum 420 a fadin kasar.

Da misalin karfe 11.43 na ranar Lahadi da daddare, NCDC ta sanar da cewa an gano karin sabbin mutane 403 da cutar ta harba a fadin Najeriya.

Sabbin mutane 403 da cutar ta harba cikin jihohin 20 sun kasance kamar haka:

Gombe-73, Legas-68, Kano-46, Edo-36, Abuja-35, Nasarawa-31, Kaduna-17, Oyo-16, Abia-15, Delta-13, Borno-13, Filato-8, Neja-7, Rivers-7, Enugu-6, Ogun-6, Kebbi-3, Ondo-1, Anambra-1, Imo-1.

Har ila yau jihar Legas ce a kan sahu na gaba ta fuskar yawan mutanen da cutar ta harba, sai jihar kuma birnin Abuja a mataki na biyu yayin da jihar Kano ta biyo bayansu a mataki na uku.

KARANTA KUMA: Har yanzu buɗe makarantu akwai haɗari - PTF

Ga jerin adadin mutanen da suka kamu da cutar a kowace daya daga cikin jihohi 35 na Najeriya da ta bulla:

Lagos-7,103;

Kano-1,137;

Abuja-1,247;

Ogun-559;

Gombe-410;

Osun-50;

Katsina-414;

Borno-438;

Edo-580;

Oyo-507;

Kaduna-446;

Bauchi-410;

Akwa Ibom-48;

Kwara-150;

Sokoto-132;

Ekiti-30;

Ondo-64;

Rivers-489;

Delta-267;

Taraba-18;

Jigawa-317;

Enugu-57;

Niger-56;

Abia-166;

Zamfara-76;

Benue-34;

Anambra-65;

Adamawa-42;

Plateau-156;

Imo-136;

Bayelsa-32;

Ebonyi-162;

Kebbi-57;

Nasarawa-172;

Yobe-55;

Kogi-3.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel