PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi

PDP ta zargi APC da yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi

Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, PDP, ta sake yin tir gami da Alla-wadai dangane da yadda matsalar rashin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a kasar nan.

PDP ta yi zargin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatinsa ta jam'iyyar APC sun yi wa lamarin tsaro rikon sakainar kashi.

Jam'iyyar ta bayyana damuwa matuka dangane da yadda 'yan ta'adda ke zubar da jinin 'yan Najeriya a Katsina, Zamfara, Sakkwato, Borno, Kaduna, Kogi, Taraba da sauran sassa a fadin kasar.

Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, PDP ta bayyana damuwarta cikin wata sanarwa da kakakinta na kasa, Kola Ologbondiyan ya fitar a ranar Lahadi cikin birnin Abuja.

PDP ta ce "tana jin radadin halin tsoro da zalunci da 'yan kasar nan ke fuskanta a hannun 'yan daban daji, masu tayar da kayar baya da kuma masu garkuwa da mutane a sakamakon gazawar gwamnatin APC."

Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan
Hakkin mallakar hoto; Jam'iyyar PDP
Kakakin jam'iyyar PDP na kasa; Kola Ologbondiyan Hakkin mallakar hoto; Jam'iyyar PDP
Asali: UGC

"Gwamnatin APC ta kasa sauke nauyin da rataya a wuyanta, ta gaza inganta tsaro ta hanyar tabbatar da tsare rayuka da dukiyoyin al'umma."

"Babban abin takaici shi ne yadda gwamnatin APC ke ikirarin ta na batar da kudi kan sha'anin tsaro amma kullum lamarin sai ci gaba da tabarbarewa ya ke."

“Abinda ya ma fi zama babban takaici shi ne yadda 'yan daban daji ke cin karensu babu babbaka sakamakon gazawar gwamnatin APC da har su ke iya kai hare-hare jihar Katsina da ta kasance mahaifar Shugaban kasa."

KARANTA KUMA: Dakarun ketare sun fi samun nasara a kan mayakan Boko Haram fiye da na Najeriya - NST

"Muna kira ga 'yan Najeriya da su lura cewa, har kawo yanzu gwamnatin APC ta gaza yin bayani kan masu tayar da zaune tsaye da ta shigo da su daga kasashen da ke makwabta da Najeriya musamman Chadi da Jamhuriyyar Nijar domin su hana ruwa gudu yayin babban zabe na 2019."

Jam'iyyar mai adawa ta ce gwamnatin APC ta gaza bijiro da matakai na kawo karshen masu tayar da kayar baya face bayar da sakonnin ta'aziya akai-akai bayan kowane mummunan hari da aka kai kan al'umma.

PDP ta janyo hankalin shugaban kasa da ya tashi ya farga "kuma ya farka daga baccinsa domin maido da tsarin ingantaccen tsaro a kasar."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel