Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya

Covid-19: Hukumar WAEC ta fadi lokacin zana jarabawar bana a Najeriya

- Hukumar shirya jarawabar WAEC ta ce a shirye ta ke wajen gudanar da jarabawar bana a dukkanin makarantun sakandire da ke fadin Najeriya

- Sai dai ta ce hakan ba zai tabbata ba har sai Gwamnatin Tarayya ta ba da izinin bude makarantu

- WAEC ta ce ko da an koma makarantu, ba za ta yi gaggawar gudanar da jarabawar ba

Duk da yadda annobar cutar korona da dagula lamura da lissafi, Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta Yammacin Afrika WAEC, ta shirya gudanar da jarabawar a bana.

Furucin hakan ya fito ne daga bakin Kakakin Hukumar, Demianus Ojijeogu, yayin ganawa da manema labarai a ranar Lahadi, 7 ga watan Yuni.

Hukumar za ta fara gudanar da jarabawa a bana da zarar Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da izinin bude makarantu a fadin kasar kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Tun a watan Maris, Hukumar WAEC ta jingine shirinta na fara gudanar da jarabawar a bana, biyo bayan rufe kafatanin makarantu a fadin kasar yayin da gwamnati ta shimfida dokar kulle.

Mista Demianus ya bayyana cewa, Hukumar a shirye ta ke ta fara gudanar da ayyukan da ta saba gudanarwa a kowace shekara, sai da ya ce ba ta cikin wani hanzari na aiwatar da hakan.

Dalibai yayin zana jarabawar WAEC
Dalibai yayin zana jarabawar WAEC
Asali: UGC

Ya ce da zarar gwamnati ta ba da izinin bude makarantu kuma dalibai sun koma aji, Hukumar WAEC za ta shimfida matakai da ka'idodin gudanar da jarabawar a bana.

Ya na fatan cewa, Hukumar ba za ta hurawa dalibai wutar gaggauta gudanar da jarabawar ba duk da ta riga da yi musu tanadin kayayyakin karatu ta hanyar yanar gizo.

KARANTA KUMA: NAPTIP ta fitar da sunayen masu cin zarafin mata a Najeriya

Ya ce WAEC za ta fitar da sabon jadawalin lokutan gudanar da jarabawar kuma yana da tabbacin sabon jadawalin zai ba dalibai isasshen lokacin da za su shirya.

Haka kuma, za a bai wa malamai da shugabannin makarantu isasshen lokacin da za su kammala shirye-shiryensu gabanin jarabawar.

Ya ci gaba da cewa, don neman kulawa da lafiyar dalibai da sauran masu ruwa da tsaki, WAEC za ta ba gwamnati damar tanadar amintattun cibiyoyi da makarantun gudanar da jarabawar.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Legit.ng ta ruwaito cewa, biyo bayan barkewar annobar korona a fadin duniya, Gwamnatin Najeriya ta dakatar da gudanar da jarabawar kammala karatun sakandire ta bana har sai mama ta gani.

Karamin ministan ilimi, Emeka Nwajubu, shi ne ya ba da sanarwar hakan cikin birnin Abuja tun a ranar Talata, 21 ga watan Afrilu, yayin bayyana taswirar gwamnati kan tsarin karatu a kasar yayin da ake fama da annoba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel