Yanzu-yanzu: Babban lauyan Najeriya, Badejo, ya yanke jiki ya fadi ya mutu
- Najeriya ta yi rashin manyan lauyoyi biyu a ranar Juma'a; Sir Jadegoke Adebonajo Badejo (SAN) da Sir Alfred Oghogho Eghobamien
- Badejo ya yanke jiki ya fadi yayin da yake fita daga gidansa a ranar Juma'a dom zuwa wurin aiki
- A yau Asabar, 6 ga watan Yuni ne kungiyar manyan lauyoyin Najeriya ta sanar da mutuwar a wata takardar ta'aziyya da ta fitar
Jadegoke Adebonajo Badejo babban lauyan Najeriya ne wanda ya yanke jiki ya fadi a yayin da yake fita daga gidansa a ranar Juma'a, 5 ga watan Yuni.
Badejo shine babban mai hannun jari a Bonajo Badejo & Co, ya rasu yana da shekaru 61 a duniya, jaridar The Nation ta ruwaito.
"Ya shirya tsaf don fita daga gida. Yana kokarin fita aiki ne a jiya da ya yanke jiki ya fadi kuma ya mutu a take," in ji wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta.
Legit.ng ta gano cewa, Badejo ya kammala karatunsa na zama babban lauya a 1980.
Ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Ife wacce a yanzu ake kira da jami'ar Obafemi Awolowo da kuma digirinsa na biyu a jami'ar jihar Legas.
A dayan bangaren, Alfred Oghogho Eghobamien ya rasu a ranar Juma'a yana da shekaru 85.
Eghobamien mahaifi ne ga Osaro Eghobamien wanda shi ma babban lauya ne.

Asali: UGC
KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi
Ya zama cikakken lauya a shekarar 1972. Ya samu mukamin zama babban lauyan Najeriya a 1995.
A yau Asabar, 6 ga watan Yunin 2020 ne kungiyar manyan lauyoyin Najeriya ta fitar da sanarwa dauke da ta'aziyyar mutuwarsu.
A ta'aziyyar Badejo, sakataren BOSAN, Seyi Sowemimo ya ce: "Muna jimamin sanar da mutuwar abokin aikinmu. Muna fatan Ubangiji ya bai wa iyalansa hakurin jure rashinsa.
"Shirye-shiryen birneshi zasu fito daga iyalansa kuma za a sanar."
A yayin jajanta mutuwar Eghobamien, Ya ce: "A matsayinsa na babban lauya a harkar siyasar jihar Edo, Eghobamien ya wakilci jihar a taron CONFAB na 2005."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng