Zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi: SERAP ta kai karar Buhari Majalisar Dinkin Duniya

Zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi: SERAP ta kai karar Buhari Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Najeriya, ta shigar da bukatar gaggawa zuwa ga Majalisar Dinkin Duniya kan kwaskwarimar da aka yiwa kasafin kudin kasar nan na bana.

Kungiyar ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta shiga lamarin, wanda take ganin hukuncin da Gwamnatin Najeriya ta yanke ya yi hannun-riga da dai-dai.

SERAP ta aike da kiran gaggawa zuwa ga wakilai 3 na musamman na Majalisar Dinkin Duniya, tana kira da su hanzarta sauya haramcin da aka aiwatar a kasafin kudin kasar nan na bana.

Ta ce akwai mafi kololuwar rashin daidaito na zaftare kasafin kudin sashen harkar ilimi da kuma na kiwon lafiya a sauye-sauyen da Gwamnatin Najeriya ta yi wa kasafin kudin kasar.

Ta kuma yi kira ga wakilan Majalisar Dinkin Duniya da su dakatar da Gwamnatin Najeriya da suke shirin batar da naira biliyan 27 wajen gyara gine-ginen Majalisar Dokoki ta Tarayya.

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da SERAP ta nemi su shiga lamarin sun hadar da; Ms. Koumbou Boly Barry, mai lura da hakkokin ilimi; Mr. Dainius Puras, mai lura da hakkokin kiwon lafiya.

Sai kuma Mr. Olivier De Schutter, wakili na musamman mai lura da hakkokin da suka shafi talauci da kuma hakkokin bil Adama.

Gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudi na naira biliyan 37 domin gyara ginin majalisar dokokin tarayyar kasar zuwa naira biliyan 27.7.

Gwamnatin Najeriya yayin gabatar da tsarin kwaskwarimar da ta yi wa kasafin kudin kasar na bana a ranar Talata, ta yanke naira biliyan 9.3 daga kasafin kudin gyara ginin majalisun tarayya.

Tun a bara, naira biliyan 37 da aka sanya cikin kasafin kudin Najeriya na bana domin gyara ginin majalisun dokokin tarayya, ya janyo cece-kuce gami da suka daga bangarori da dama a fadin kasar.

Galibin 'yan Najeriya suna cewa wannan ba komai ba ne illa barnar kudi da almundahana sannan kwata-kwata ba ya kan tsarin lura da halin da ake ciki.

Sai dai a yanzu 'dole kanwar naki' ta jefa gwamnatin cikin dogon nazari tare da yin bita a kan kasafin kudin kasar na bana da shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu tun a bara.

Biyo bayan karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da kuma hasashen raguwar kudaden shiga da gwamnati za ta samu, ya sanya ta zaftare wani kaso daga kasafin da ta kiyasta.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai; Femi Gbajabiamila
Shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da Shugaban Majalisar Dattawa; Sanata Ahmed Lawan, da kuma Kakakin Majalisar Wakilai; Femi Gbajabiamila
Asali: UGC

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya mika wa majalisun dokoki na tarayya sabon kudirin yi wa kasafin kudin kasa kwaskwarima, kuma kudirin ya na kan gaba ta karatu na biyu a majalisun.

Buhari ya yi bayanin cewa, kwaskwarimar ta zama dole saboda faduwar farashin mai da kuma rage adadin danyen mai da kasar ke fitar wa, wanda duk annobar cutar korona ce ta haddasa.

A sabon kudirin yi wa kasafin kudin kasar na bana kwaskwarima, ga sauyin da za a yi wa kasafin kudin Majalisar Dokoki ta Tarayya, Ma'aikatar lafiya da kuma Ma'aikatar ilimi:

An yanke kashi 25.1 cikin 100 daga naira biliyan 37 da aka sanya za a gyara ginin Majalisar Dokoki, inda a yanzu adadin kudin ya koma naira biliyan 27.7.

KARANTA KUMA: Cutar korona ta hallaka mutum 7 a jihar Gombe - Prof. Idris Mohammed

Sai kuma asusun kananan ma'aikatun kiwon lafiya na kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar, an zaftare kashi 42.5 cikin dari, daga naira biliyan 44.5 zuwa naira biliyan 25.5 kacal.

Haka zalika, an rage kashi 54.25 cikin dari na kasafin kudin hukumar kula da karatun bai-daya UBE, daga naira biliyan 111.7 zuwa naira biliyan 51.1.

Cikin bukatar gaggawa da ta shigar, mataimakin shugaban kungiyar SERAP, Kolawole Oluwadare, ya ce Gwamnatin Najeriya tana fifita alawus da jin dadin 'yan siyasa fiye da hakkokin al'umma.

Mista Oluwadare da ya ke babatu a ranar Laraba, 3 ga watan Yuni, ya ce sauye-sauyen da aka yi wa kasafin kudin kasar ya nuna gwamnati ba ta da shirin bunkasar tattalin arzikin kasar.

Haka kuma ya ce ba ta nufin tunkarar kalubalen da kasar nan ta ke fuskanta musamman halin da annobar korona ta jefa talakawa a kasar.

Da wannan dalilai ne SERAP ta ke neman Majalisar Dinkin Duniya ta hurowa Gwamnatin Najeriya wutar jingine hukunce-hukuncen da ta yi wa kasafin kudin kasar.

Ta bukaci a sanya matsin lamba kan Gwamnatin, domin ta sauka daga kudirin rage kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi.

A karshe ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da kasafin naira biliyan 27 da ta ware domin gyara ginin Majalisar Dokokin Tarayya ya koma zuwa kasafin Ma'aikatar Ilimi da ta Lafiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel