Gwamnatin Tarayya ta zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi

Gwamnatin Tarayya ta zaftare kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi

- Gwamnatin Najeriya ta aiwatar da manyan sauye-sauye a kwaskwarimar da ta yi wa kasafin kudin kasar na bana

- Gwamnatin kasar ta zaftare babban kashi daga cikin kasafin kudin Ma'aikatar Lafiya da ta Ilimi

- Kungiyoyi masu zaman kansu na ganin babu adalci a wani sashe na kwaskwarimar da aka yi wa kasafin kudin kasar

Rahotanni da suka bullo a ranar Talata, 2 ga watan Yuni, sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta zabtare kasafin kudin gyara ginin majalisar dokokin tarayya da kusan naira biliyan 10.

Gwamnatin tarayya ta rage kasafin kudi na naira biliyan 37 domin gyara ginin majalisar dokokin tarayyar kasar zuwa naira biliyan 27.7.

Gwamnatin Najeriya yayin gabatar da tsarin kwaskwarimar da ta yi wa kasafin kudin kasar na bana a ranar Talata, ta yanke naira biliyan 9.3 daga kasafin kudin gyara ginin majalisun tarayya.

Tun a bara, naira biliyan 37 daka sanya cikin kasafin kudin Najeriya na bana domin gyara ginin majalisu dokokin tarayya, ya janyo cece-kuce gami da suka daga bangarori da dama a fadin kasar.

Galibin 'yan Najeriya suna cewa wannan ba komai ba ne illa barnar kudi da almundahana sannan kwata-kwata ba ya kan tsarin lura da halin da ake ciki.

Sai dai a yanzu 'dole kanwar naki' ta jefa gwamnatin Najeriya cikin dogon nazari tare da yin bita a kan kasafin kudin kasar na bana da shugaba Muhammadu Buhari ya rattabawa hannu tun a bara.

Biyo bayan karyewar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya da kuma hasashen raguwar kudaden shiga da gwamnati za ta samu, ya sanya ta zaftare wani kaso daga kasafin da ta kiyasta.

A ranar Alhamis ne shugaba Buhari ya mika wa majalisun dokoki na tarayya sabon kudirin yi wa kasafin kudin kasa kwaskwarima, kuma kudirin ya na kan gaba ta karatu na biyu a majalisun.

Buhari ya yi bayanin cewa, kwaskwarimar ta zama dole saboda faduwar farashin mai da kuma rage adadin danyen mai da kasar ke fitar wa, wanda duk annobar cutar korona ce ta haddasa.

Buhari, shugaban majalisar dattawa; Sanata Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila
Buhari, shugaban majalisar dattawa; Sanata Ahmed Lawan, da kakakin majalisar wakilai; Femi Gbajabiamila
Asali: UGC

A sabon kudirin yi wa kasafin kudin kasar na bana kwaskwarima, ga sauyin da za a yi wa kasafin kudin Majalisar Dokoki ta Tarayya, Ma'aikatar lafiya da kuma Ma'aikatar ilimi:

An yanke kashi 25.1 cikin 100 daga naira biliyan 37 da aka sanya za a gyara ginin Majalisar Dokoki, inda a yanzu adadin kudin ya koma naira biliyan 27.7

Sai kuma asusun kananan ma'aikatun kiwon lafiya na kananan hukumomi 774 da ke fadin kasar, an zaftare kashi 42.5 cikin dari, daga naira biliyan 44.5 zuwa naira biliyan 25.5 kacal.

KARANTA KUMA: Najeriya ta na bayanka - Buhari ya tabbatar wa shugaban bankin Afrika, Adesina

Haka zalika, an rage kashi 54.25 cikin dari na kasafin kudin hukumar kula da karatun bai-daya UBE, daga naira biliyan 111.7 zuwa naira biliyan 51.1.

Duka duka dai an cire kashi 10 cikin 100 na kasafin kudin majalisar dokokin tarayya, daga naira biliyan 128 zuwa naira biliyan 115.2

Hakan ta ke ga ma'aikatar shari'a ta kasa, wadda ita ma aka zaftare kashi 10 cikin 100 daga kasafin kudinta. A baya an sanya mata naira biliyan 110, yayin da yanzu ya dawo naira biliyan 99.

A yayin martani game da kudirin kwaskwarimar da za a a yiwa kasafin kudin kasar na bana, wasu kungiyoyi biyu masu zaman kansu sun tofa albarkacin bakinsu.

Shugaban cibiyar yaki da rashawa CACOL, Debo Adeniran, ya ce abin takaici ne a ce an zaftare kasafin kudin bangaren lafiya da na ilimi duk da yadda talauci ya yi wa kasar nan katutu.

Haka kuma shugaban hukumar bunkasa ci gaban al'umma, Lanre Suraj, ya bayyana takaicin yadda har yanzu ba a jingine batun barnatar da kudi ba wajen gyara ginin majalisun tarayyar.

Mista Suraj, yayin babatu kan rage kasafin kudin ma'aikatar lafiya da ta ilimi, ya ce Buhari ba zai yi ikirarin cewa bai san rashin adalcin da hakan zai zamo ga 'yan Najeriya ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel