Kasashe 11 a Afrika da suka fi tara mutane masu ilimi

Kasashe 11 a Afrika da suka fi tara mutane masu ilimi

- Najeriya ba ta cikin jerin kasashe 11 wadanda suka tara mutane masu himmar karatun boko, kamar yadda shafin World Population Review ya fitar

- Cikin jerin da shafin Kididdigar Afrika (Africa Facts Zone) ya fitar a Twitter, ya nuna kasar Equatorial Guinea ta fi kowace kasa a nahiyar Afrika tara masu ilimin boko

- Kasashen da ke kasa a jerin sun hadar Zimbabwe, Estwatini da Gabon

Mujallar Africa Facts Zone, mai fitar da kididdiga kan lamuran da suka shafi nahiyar Afirka, ta wallafa jerin kasashe 11 da suka tara mafi yawan mutane masu ilimi.

A cikin jerin, kasar Equatorial Guinea, ta ja ragamar tara dimbin al'umma masu ilimi da kashi 95 cikin 100. Sai kuma kasar Seychelles da ta biyo baya a mataki na biyu da kashi 94 cikin 100.

Kamar yadda Africa Facts Zone ta kalato daga Hukumar Duniya mai bita a kan yawan jama'a, World Population Review, ta nuna cewa kasar Afrika Ta Kudu ce a mataki na uku da kashi 93 cikin 100.

Sai kuma kasar Libiya a mataki na hudu da kashi 90 cikin dari na adadin mutanen kasarta da suka himmatu wajen neman ilimi.

Mauritius ce a mataki na biyar, yayin da aka samu kashi 89 cikin 100 na adadin al'ummarta da suka mike tsaye wajen yakar jahilci.

Sai dai abun mamaki shi ne, yadda Najeriya ba ta shiga cikin sahun kasashen ba da suka yi zarra a fannin ilimin boko.

Abun mamakin shi ne yadda kasashe irinsu Bostwana, Zimbabwe, da kuma Gabon suka yi wa Najeriya fintinkau duk da kallon da ake mata a matsayin babban-goro cikin kasashen Afirka.

Ga dai jerin kasashen 11 da kuma kashi-kashi na mutane masu ilimi da kowannensu ya kunsa:

1. Equatorial Guinea (95%)

2. Seychelles (94%)

3. South Africa (93%)

4. Libya (90%)

5. Mauritius (89%)

6. Botswana da Burundi (87%)

8. Cape Verde (85%)

9. Zimbabwe (84%)

10. Eswatini (83%)

11. Gabon (82%).

KARANTA KUMA: Adadin masu cutar korona a Afirka ya zarta 150,000 - WHO

Hoton yadda dalibai suka himmatu wajen neman ilimi a cikin aji
Hoton yadda dalibai suka himmatu wajen neman ilimi a cikin aji
Asali: UGC

A rahoton da Africa Facts Zone ta fitar, ya nuna cewa, Aliko Dangote shi ne mahalukin da ya fi kowane mutum kudi a nahiyar Afirka, yayin da dukiyar da ya mallaka ta kai dala biliyan 9.5.

Mutum na biyu da ya fi kowa arziki a Afirka, shi ne Nicky Oppenheimer, wanda ya fito daga Afirka ta Kudu kuma ya mallaki dukiya da darajarta ta kai dala biliyan 7.5 (N2,902,500,000,000).

A mutum 8 da suka fi kowa dukumar dukiya a nahiyyar, Najeriya ta na da attajirai uku da suka hadar da Mike Adenuga da Abdussamad Rabi'u, wanda ke zaman na hudu da na takwas a jerin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel